Ziyarar Aisha Buhari wajen Atiku Abubakar Ta Jawo Abin Magana a Twitter

Ziyarar Aisha Buhari wajen Atiku Abubakar Ta Jawo Abin Magana a Twitter

  • Matar tsohon shugaban Najeriya, Aisha Buhari da wasu mutanenta sun ziyarci Atiku Abubakar a Adamawa
  • Alhaji Atiku Abubakar ya yi amfani da wannan ziyara, ya koka game da halin da ‘yan Najeriya suke ciki
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya dade yana kuka da manufofin APC, yana cewa sun jefa jama’a a kunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Adamawa - Tsohuwar uwargidar Najeriya, Aisha Buhari ta ziyarci Atiku Abubakar da ke neman zama shugaban kasa.

Atiku Abubakar wanda jagoran adawa ne a Najeriya yana neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC a zaben 2027.

Aisha Buhari
Aisha Buhari da mutanenta a gidan Atiku Abubakar da tshon mataimakin shugaban kasar a zaune Hoto: @Atiku
Source: Twitter

An ga Aisha Buhari wajen Atiku Abubakar

Hotuna daga shafin Atiku Abubakar a X sun tabbatar da ziyarar da Hajiya Aisha Buhari ta kai wa ‘dan takaran adawar.

Da yake magana a ranar Laraba, ya yi alkawarin gina tattalin arziki ta yadda kowa zai rayu cikin kima da raja a Najeriya.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta ziyarci Atiku ana maganar siyasar 2027

Aisha Buhari da Atiku wanda ya rike sarautar Wazirin Adamawa duk sun fito ne daga jiha guda.

Atiku Abubakar game da ziyarar Aisha Buhari

Atiku ya ce:

“Yau na yi farin cikin karbar tsohuwar uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari. Na ji dadi kuma na yi matukar yaba wa ziyararta.
Baya ga zumuncin da aka yi, tunatarwa ce a gare mu game da nauyi ne gadan-gadan da yake gabanmu gaba daya mu da ke son ganin Najeriya ta yi kyau: mu sa walwala, daraja da kuma makomar al’ummarmu a farko.

Daga nan ya buge da cewa iyalai suna shan wahala saboda tsadar abinci da kudin zirga-zirga a mulkin Mai girma Bola Tinubu.

'Dan takarn ADC ya kuma koka da cewa kudin magani da sauran abubuwan more rayuwa sun yi tsada.

Abin da jama'a suke fada a dandalin X

Ganin yadda ya kawo siyasa a ziyarar, yana alkawarin zai kawo talaka sauki idan ya ci zaben 2027 ya jawo surutu a shafin X.

Shafin magoya bayan ADC mai suna ADC Vanguard ya yi ikirarin Arewa ta dunkule tana tare da ‘dan takaranta na 2027.

Kara karanta wannan

Matsala ga Tinubu: Ana ganin Atiku zai lashe jihohi 19 a Arewa da 3 a Kudu a zaben 2027

Sambo Mai Hula wanda yana tare da APC ya rubuta:

/Dariya/
Shi Atiku dole sai ya siyasantar da komai ne? Aisha Buhari ta kai wa mutumin jiharta, dattijon kasa ziyara ne kawai, amma Baba Atiku yana neman kawo siyasa a ziyar tata.
Shin yana tunanin akwai tasirin Baba Buhari ta wurinta ne ko mene ne? Shugaba Bola Tinubu ya hana ‘yan adawa sakat domin suna son amfani da kowace irin dama da sunan ana goyon bayansu

“Wannan ba ziyarar yau da kullum ba ce, sako ne tsohuwar shugaban kasar ta ke aika wa Tinubu.” - Ghata 01

Yusuf.io ya yi hasashen APC za ta sha kashi a zaben badi, yana mai kamanta tafiyar Bola Tinubu da ta Goodluck Jonathan a 2015.

Wannan shi ne ra’ayin Mikano Identity:

“A yadda ake tafiyar nan, idan Tinubu bai nemo mafita ba, Atiku zai lashe zabe tun kafin a fara.”

Shi wani mai suna @Giftedhandy bai ga abin tada hankalin APC da wannan ziyara ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kira wa kansa ruwa bayan neman Atiku ya hakura da takara a 2027

Tun da ya ga Aisha Buhari wajen Atiku Abubakar, @M3onsight ya tabbatar da cewa ba zai zabi ‘dan takaran na ADC ba.

Nikee ya zargi gwamnatin mai gidan Aisha Buhari da lalata tattalin arzikin Najeriya, ya ce amma an bar Tinubu da shan suka.

“Ta tabbata yanzu iyalin tsohon shugaban kasa Buhari suna goyon bayan Atiku ne”

- @AT_Sadeeq

@Didi_okoh ya ba shugaba Tinubu shawara da kada ya yi wasa da gwamnonin APC, ya ce siyasar Arewa dabam ta ke.

Shi Malam Muhammad Makintamie shi tambaya yake yi ko Aisha Buhari za ta goyi bayan su (ADC) a 2027.

Machala cewa yake yi ko da kudi ko babu, za su tallata Atiku a 2027

Adamsi012 bai yarda da ita ba, yake cewa:

"Ba da dadewa ba za ta sa kayan Omo Logo, ta yi wa Bola Tinubu kamfe."

Bulama D’Great kuma yake nuna cewa tafiya ta yi tafiya.

Wani mai suna Oba Of Port Harcourt ya rubuta:

"Kaka ‘dan shekara 80 wanda ya gaji ba zai iya jure wahalar mulkin Najeriya ba. Ka yi ritaya. Atiku ba zai taba zama shugaban Najeriya ba."

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari ya fadi sirri da ya kama aikin tallar Tinubu babu kama hannun yaro

A cewar Kwamred Abdulaziz Adamu CAA, sako ya isa da kyau.

HAHayatu ya ce:

“Ai naka sai naka”

Masoyin Wazirin Adamawa, Abdulaziz Na’ibi ya ce:

Arewa za ta koya wa Tinubu darasi cewa mulki na jama’a ne. 2027 ne karshen APC.

Dalung ya ce ADC za ta doke Bola Tinubu

Labari ya gabata cewa tsohon ministan wasanni da matasa a 2015, ya leka zaben 2027 ya gano za a dankara Bola Ahmed Tinubu da kasa.

Solomon Dalung ya yi hasashen Bola Tinubu zai sha mummunan kaye a zaben 2027 saboda mutuwar Muhammadu Buhari za ta taba APC.

Ya kuma ce wahalar da 'yan arewa suke ci kadai ta isa ta yi wa jam'iyyar adawa kamfe, ta jawo mutane su ki zaben 'dan takaran APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng