Dangote Ya Dawo Sayar da Fetur da Naira, Ya Sauya Farashin Litar Mai

Dangote Ya Dawo Sayar da Fetur da Naira, Ya Sauya Farashin Litar Mai

  • Matatar Dangote ta koma sayar da fetur da Naira bayan dakatar da tsarin na ɗan lokaci tare da fara amfani da Dalar Amurka
  • Kamfanin ya ƙara farashin man fetur daga N1,075 zuwa N1,215 kan kowace lita, wanda ya nuna ƙarin N140, hakan ya nuna karin 13%
  • Masu harkar mai sun ce sabon matakin ya kawo ƙarshen damuwar da tsarin biyan kuɗi da Dala ya haifar a kasuwar man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Legas – Matatar Dangote ta koma sayar da man fetur da Naira bayan ta dakatar da tsarin na ɗan lokaci tare da amfani da Dala wajen cinikin cikin gida.

Sai dai dawowar ta zo ne tare da ƙarin farashin fetur, inda aka ɗaga farashin daga N1,075 zuwa N1,215 kan kowace lita, wanda ya nuna ƙarin N140 ko kuma 13.02%

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

Alhaji Aliko Dangote da matatar shi
Aliko Dangote a hagu da matatar shi a dama. Hoto: Getty Images|Dangote Industries
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa wannan mataki ya kawo ƙarshen tsarin biyan kuɗi da Dala da matatar ta fara makon da ya gabata, wanda ya jefa kasuwar man fetur cikin rashin tabbas.

Sabon farashin ya fara aiki

A cikin wata sanarwa da sashen kasuwanci na matatar ya aikewa masu sayen mai, an bayyana cewa sabon farashin ya fara aiki daga ranar 22 ga Yulin 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa:

"Muna sanar da ku cewa duk man fetur da ba a ɗauka ba zai kasance ƙarƙashin sabon farashin da ya fara aiki daga ranar 22 ga Yuli, 2026.
"Ku ci gaba da yin odarku. Idan kuna buƙatar ƙarin bayani, ku tuntube mu."

Haka kuma, an ƙara farashin jigilar fetur ta teku daga N1,441,575 zuwa N1,602,495 kan kowane ton.

Dalilin da ya sa aka koma Naira

Shafin Petroleumprice.ng ya tabbatar da cewa matatar ta koma amfani da naira wajen sayar da fetur ga kasuwar cikin gida.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana bayan ganin kumfa a Kaduna

Babban Jami'in Kamfanin, Jeremiah Olatide, ya ce an sanar da kwastomomi cewa an dawo da tsarin sayar da fetur da naira tare da sabon jadawalin farashi.

A lokacin da matatar ta koma amfani da dala, farashin fetur a manyan rumbunan mai masu zaman kansu ya tashi daga kusan N1,075 zuwa N1,275 kan kowace lita.

Masu kasuwancin mai masu zaman kansu sun dakatar da ɗaukar mai daga matatar saboda rashin samun isassun Dalar Amurka domin biyan kuɗi.

Ana sayen man fetur a Najeriya
Mutane na layin shan man fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Masana sun yi gargaɗi kan

Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur sun yi gargadin cewa ci gaba da amfani da Dala zai ƙara buƙatar kuɗin waje, ya raunana darajar Naira tare da haifar da ƙarin tashin farashin fetur a faɗin ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa idan tsarin ya ci gaba, masu kasuwanci za su riƙa buƙatar kusan Dala miliyan 40 a kowace rana domin sayen fetur daga matatar.

Wannan na nufin za a kashe sama da dala biliyan 14 a shekara wajen sayen fetur kawai.

Matatar Dangote ta bayyana cewa ta koma amfani da dala ne saboda ƙarancin ɗanyen mai da take samu a ƙarƙashin shirin gwamnati na musayar ɗanyen mai da Naira, lamarin da ya tilasta mata sayen ƙarin ɗanyen mai daga kasuwar duniya da Dala.

Kara karanta wannan

Mai shekara 60 ya rasu bayan zuwa otel da budurwa, an samu maganin jima'i

Dangote na so a tona asirin direbobi

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin Dangote ya ƙaddamar da wani shiri na bai wa masu tona asirin masu amfani da motocinsa ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin ya ce shirin ba wanda ya tona asiri N500,000 na da nufin dakile amfani da manyan motocinsa wajen jigilar kayayyaki ko mutane ba tare da izini ba.

Dangote ya buƙaci jama'a su rika kai rahoton duk wani motsi da suke zargin ya saɓa wa dokokin amfani da motocin kamfanin domin kare mutuncin harkokin sufuri na kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng