Bayani Dalla Dalla kan Yadda za Ku Saye Hannun Jari a Matatar Dangote
- Matatar Dangote za ta fara sayar da hannun jari ga jama’a a ranar Litinin, 14 ga Satumban 2026, inda ‘yan Najeriya za su samu damar mallakar kaso a kamfanin
- Hannun jarin da za a sayar sun kai biliyan 4.1, inda aka sanya farashin guda ɗaya a N525, yayin da ake sa ran za a tara kusan N2.15tn domin faɗaɗa matatar
- Mafi ƙarancin hannun jarin da mutum zai iya saya guda 10 ne, wanda zai kashe N5,250, domin bai wa talakawa da ma’aikata damar zama masu hannun jari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Matatar Dangote za ta buɗe babbar damar sayar da hannun jari ga jama’a a ranar Litinin, 14 ga Satumban 2026, a wani mataki da zai bai wa ‘yan Najeriya damar mallakar kaso a matatar.
Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanya hannu kan takardun sayar da hannun jarin a wani biki da aka gudanar a Eko Hotels and Suites da ke Victoria Island, Lagos, ranar Litinin, 7 ga Satumba.

Source: Facebook
Bayanin matatar Dangote
A sakon da kamfanin Dangote ya wallafa a Facebook ya ce za a sayar da hannun jari biliyan 4.1 a farashin N525 kowanne, inda kamfanin ke sa ran tara kusan N2.15tn
Kuɗin zai taimaka wajen gudanar da shirin faɗaɗa matatar, wanda zai kusan ninka ƙarfin samar da ita zuwa ganga miliyan 1.4 na ɗanyen mai a kowace rana.
1. Buɗe asusun hannun jari
Mutumin da ke son sayen hannun jarin kamfanin a kasuwar hannun jari ta Najeriya zai bukaci yin hakan ta hannun kamfanin dillalan hannun jari da hukumomin da suka dace suka amince da shi.
Idan ba ka da asusun cinikin hannun jari, za ka buƙaci buɗe ɗaya tare da wani dillali da Hukumar Kula da Kasuwannin Hannun Jari ta Najeriya (SEC) da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya (NGX) suka amince da shi.
Yawancin dillalai yanzu suna ba da damar yin rajista ta intanet, inda ake buƙatar lambar tantancewa ta banki (BVN), takardar shaida mai inganci da hoton fasfo domin tantance mutum.
Kafin saka kuɗi, ya dace mai saka hannun jari ya tabbatar da cewa dillalin da yake son amfani da shi yana da rajista a hukumance.
2. Buɗe asusun CSCS
Ba a bayar da hannun jari da takardar mallaka ta zahiri, domin ana adana su ta hanyar lantarki a tsarin CSCS.
Idan mutum ya buɗe asusun cinikin hannun jari, dillalinsa zai iya buɗe masa asusun CSCS ko kuma ya haɗa shi da wanda yake da shi.
Hannun jarin da aka ware wa mai saka hannun jari za a shigar da su kai tsaye cikin asusunsa na CSCS bayan fara cinikinsu.
3. Kammala tantance bayanan mutum
Dillalin hannun jari zai nemi wasu takardu domin tabbatar da bayanan mai saka hannun jari da kunna asusunsa kafin ya iya neman hannun jarin.
Abubuwan da ake buƙata na iya bambanta daga wani dillali zuwa wani, don haka ana buƙatar mai saka hannun jari ya bi jerin takardun da dillalinsa ya tanada.
4. Sanya kuɗi a asusun
Bayan an bude asusun, mai saka hannun jari zai saka kuɗin da yake shirin amfani da shi wajen neman hannun jarin.
A farashin N525 kan kowane hannun jari, mafi ƙarancin guda 10 zai ci N5,250. Ana buƙatar mai saka hannun jari ya tabbatar da cewa kuɗinsa a shirye suke kafin ranar buɗe sayar da hannun jarin.
5. Jira ranar fara sayarwa
Za a buɗe damar neman hannun jarin a ranar 14 ga Satumba, 2026, kuma ana sa ran za a rufe ta ranar 13 ga Oktoba, 2026.
Masu saka hannun jari ya kamata su dogara da takardun sayar da hannun jarin da aka amince da su domin samun ainihin ranakun, tsarin neman hannun jarin da sauran bayanai.

Source: Getty Images
6. Sayen hannun jarin
Ana sa ran masu neman hannun jarin za su gabatar da buƙatunsu ta hannun dillalan hannun jari da aka amince da su da kuma sauran hanyoyin da aka bayyana a cikin takardun sayar da hannun jarin.
Mai saka hannun jari zai bayyana adadin hannun jarin da yake son saya, ya sake duba bayanansa sannan ya gabatar da buƙatarsa kafin ranar rufewa.
Punch ta wallafa cewa ya kamata a guji bai wa mutanen da ba a tabbatar da sahihancinsu ba kuɗi domin sayen hannun jarin.
7. Jiran raba hannun jari
Gabatar da buƙatar sayen hannun jari ba yana nufin za a samu duk adadin da aka nema ba.
Idan mutane da yawa sun nemi hannun jarin fiye da adadin da ake da shi, ana iya rage adadin da za a bai wa kowane mutum, sannan a mayar da sauran kuɗin da bai samu hannun jari ba bisa tsarin da aka tanada.
Idan an ware maka hannun jari, za a shigar da shi cikin asusunka na CSCS.
8. Bibiyar kamfanin
Bayan an fara cinikin hannun jarin a Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya, mai saka hannun jari zai iya bibiyar darajarsa ta hanyar manhajar ko tsarin ciniki na dillalinsa.
Farashin hannun jarin zai iya hawa ko sauka bisa yadda kamfanin yake gudanar da ayyukansa, ra’ayin masu saka hannun jari da yanayin kasuwa.
Masu hannun jari za su iya riƙe hannun jarin na dogon lokaci ko kuma su sayar da shi ta hannun dillalinsu idan farashin kasuwa ya dace da su.
Maganar tallafin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ƙungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin man fetur domin rage tsadar rayuwa a Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa buƙatar na cikin wata takardar da shugaban ƙungiyar, Andrew Emelieze, ya sanya wa hannu ranar Litinin.
Ƙungiyar ta kuma bukaci a samar da alawus na tsadar rayuwa na dindindin tare da aiwatar da kashi 40 cikin 100 na alawus na musamman da sauransu.
Asali: Legit.ng




