Rassan Bankuna 476 Sun Rufe a Kano, Kaduna da Sauran Jihohi

Rassan Bankuna 476 Sun Rufe a Kano, Kaduna da Sauran Jihohi

  • Bankunan Najeriya sun rufe rassa da cibiyoyin hada-hadar kudi 476 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025 a bayanan da Babban Bankin Najeriya ya nuna
  • Adadin rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi ya ragu daga 5,410 a shekarar 2022 zuwa 4,934 a 2025, wanda ke nuna raguwar kashi 8.8 cikin 100
  • Raguwar ta fi kamari a shekarun 2024 da 2025, inda aka rufe wurare 439, yayin da Lagos ta kasance jihar da ta fi rasa rassan bankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Bankunan Najeriya sun rufe rassa da cibiyoyin hada-hadar kudi 476 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025, lamarin da ya rage yawan wuraren da bankuna ke gudanar da ayyukansu da kashi 8.8 cikin 100.

Bayanan da ke cikin kundin kididdigar bangaren hada-hadar kudi na CBN na shekarar 2025 sun nuna cewa rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi sun ragu daga 5,410 a 2022 zuwa 4,934 a 2025.

Kara karanta wannan

An lissafa tiriliyoyin kudin da za a kashe idan aka maido tallafin man fetur

Bankin CBN na Najeriya
Babban bankin Najeriya na CBN. Hoto: CBN
Source: Facebook

Bankuna sun rufe rassa 476

Punch ta yi nazarin bayanan CBN, inda ta gano cewa an samu raguwar rassa 37 daga 5,410 a 2022 zuwa 5,373 a 2023.

A shekarar 2024 kuma, adadin ya ragu da wasu wurare 229 zuwa 5,144, kafin bankuna su sake rufe wurare 210 a 2025.

Hakan na nufin kusan kashi 92 cikin 100 na raguwar wurare 476 da aka samu cikin shekaru ukun ya faru ne a 2024 da 2025.

CBN ta ce bayanan sun kunshi rassan bankunan kasuwanci, bankunan ’yan kasuwa da bankunan da ba sa karbar kuɗin ruwa.

Lagos ta fi rasa rassan bankuna

Rahoton ya bayyana cewa jihar Lagos ce ta fi fuskantar raguwar rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi.

Jihar tana da wurare 1,602 a 2022, amma adadin ya ragu zuwa 1,532 a 2023, sannan 1,521 a 2024 kafin ya koma 1,444 a 2025.

Wannan na nufin an rufe wurare 158 a jihar cikin shekaru uku, wanda ya yi daidai da raguwar kashi 9.9 cikin 100.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Dangote ya fara sayar da hannun jarin matatar shi

Duk da raguwar, Lagos ta ci gaba da kasancewa cibiyar harkokin banki, inda take da kusan kashi 29 cikin 100 na dukkan rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi 4,934 da ke Najeriya a 2025.

Abuja da Ekiti sun fuskanci matsala

Babban Birnin Tarayya Abuja ma ya samu raguwar rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da dama.

Adadin wuraren da bankuna da cibiyoyi suke sun kai 400 a 2022 da 2023, kafin ya ragu zuwa 391 a 2024 da kuma 362 a 2025.

Hakan ya nuna an samu raguwar wurare 38, wato kashi 9.5 cikin 100 cikin shekaru uku da suka gabata.

Ekiti ta fuskanci daya daga cikin mafi girman raguwar, inda adadin wuraren ya kusan rabi, daga 107 a 2022 zuwa 57 a 2025.

A daya bangaren, Enugu ta rasa wurare 44, daga 162 zuwa 118, yayin da Oyo ta rasa 41, daga 237 zuwa 196.

Me ya Kano da Kaduna?

Kano ta samu karin rassan bankuna a farkon lokacin, inda adadin ya tashi daga 164 a 2022 zuwa 175 a 2023 da 183 a 2024.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa adadin ya fadi sosai a 2025 zuwa 157, wanda ke nufin jihar ta rasa wurare 7 idan aka kwatanta da 2022.

Kara karanta wannan

Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Kaduna ma ta bi irin wannan tsari, inda adadin ya karu daga 148 a 2022 zuwa 156 a 2023 da 164 a 2024, kafin ya koma 146 a 2025.

Wasu jihohi kuwa sun samu karin rassan bankuna. Delta ta kara wurare 23, daga 173 zuwa 196, yayin da Edo ta tashi daga 155 zuwa 165.

Dangote na sayar da hannun jari

A wani labarin, mun ruwaito cewa hamshakin attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya fara sayar da hannun jarin matatar shi, a wani kaso na sayar da hannun jari mafi girma da aka taba samu a Afirka.

An bude damar sayen hannun jarin ga kananan masu zuba jari, inda kamfanin ya fitar da hannun jari biliyan 4.1 kan N525 kowanne.

Idan aka sayi dukkan hannun jarin, ana sa ran sayarwar za ta tara N2.15trn, yayin da kudin za a yi amfani da su wajen fadada matatar da sauran shirye-shiryen kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng