Shari'ar da Za Ta Yanke Makomar Shugabancin ADC Ta Gamu da Cikas a Kotu
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron karar da ke neman hana David Mark da wasu jagororin ADC gudanar da harkokin jam’iyyar
- An dage sauraron karar zuwa 28 ga Satumba saboda alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Peter Lifu, bai zauna a kotu ba
- Nafiu-Bala Gombe na zargin cewa kafa shugabancin Mark da Rauf Aregbesola ya saba wa kundin tsarin ADC da dokar zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron karar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar, inda yake neman hana David Mark da shugabannin jam’iyyar ADC gabatar da kansu a matsayin jagororin jam’iyyar.
An dage ci gaba da shari’ar zuwa 28 ga Satumba, bayan alkalin da ke sauraron karar, Mai Shari’a Peter Lifu, bai zauna a kotu ba ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2027.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Source: Facebook
An shirya zaman ne domin sauraron dukkan wasu buƙatun da ke gaban kotun dangane da karar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Alƙali ya ki janye kansa daga shari’ar
Alkalin kotun, mai shari’a Lifu ya sanya ranar 16 ga Yuni domin sauraron dukkan buƙatun da ke shari'ar bayan da ya yi watsi da bukatar a janye shi daga shari’ar.
Alƙalin ya ce buƙatun biyu da ADC da Ogbeni Rauf Aregbesola suka shigar ba su da hujjar da za ta sa ya janye kansa daga karar.
A sakamakon haka, kotun ta ci tarar ADC da Aregbesola Naira miliyan ɗaya kowannensu, tare da bai wa Nafiu Bala Gombe kudin.
ADC da Aregbesola sun nemi alƙalin ya janye daga shari’ar a wasu buƙatu daban-daban, suna zargin cewa yana nuna son kai.
Abin da Nafiu Gombe ke nema a kotu
Nafiu Bala Gombe, wanda mamba ne a ADC kuma ke nuna rashin amincewarsa da wasu matakan da aka ɗauka a jam’iyyar, ya shigar da karar ne domin neman umarnin kotu da zai hana David Mark, Aregbesola da sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na rikon kwarya (NWC) bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.
Ya yi ikirarin cewa yadda Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya suka samu shugabancin jam’iyyar ya saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ADC da kuma Dokar Zaɓe.
Waɗanda aka kai kara
Nafiu Bala Gombe ya maka ADC, David Mark, Rauf Aregbesola, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da Ralph Nwosu a matsayin waɗanda ake kara.
An yi wa karar rajista da lambar FHC/ABJ/CS/1819/2025.
Nwosu ya sauka daga shugabancin ADC
Ralph Nwosu shi ne tsohon shugaban ADC na ƙasa kafin ya sauka daga mukaminsa, lamarin da ya ba da damar kafa sabon shugabancin da David Mark ke jagoranta.
Yanzu dai ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron dukkan buƙatun da ke gaban ta a ranar 28 ga Satumba.

Source: Facebook
ADC ta shiryawa zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ta shirya fuskantar duk wani yanayi a zaɓen 2027 da ake tunkara.
ADC ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar kayar da jam’iyyar APC mai mulki idan aka gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.
Asali: Legit.ng
