China Ta Yi Magana kan Cewa Ta Taimaki Iran wajen Kashe Sojojin Amurka
- Kasar China ta musanta rahotannin cewa wasu kamfanoninta sun bai wa Iran hotunan tauraron dan Adam na wata sansanin sojin Amurka da ke Jordan
- Rahotannin sun ce an bai wa Iran hotunan ne kafin da kuma bayan harin makami mai linzami da ya kashe sojojin Amurka 3 a sansanin Muwaffaq Salti
- A bayanin da ta yi, China ta ce zargin ba shi da tushe, yayin da Donald Trump ya ce China da Amurka duk suna yi wa juna leken asiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Kasar China ta musanta rahotannin cewa wasu kamfanoninta sun bai wa Iran bayanan sirri da suka shafi wani sansanin sojin Amurka da ke Jordan.
Rahotannin sun shafi harin makami mai linzami da Iran ta kai sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti da ke Jordan a ranar 17 ga Yuli, inda sojojin Amurka 3 suka mutu.

Source: Getty Images
Martanin da China ta yi
Jaridar Wall Street Journal ta wallafa rahoton cewa wasu hukumomin Amurka da ba a bayyana sunayensu ba sun yi zargin cewa wasu kamfanonin China sun bai wa Tehran hotunan tauraron dan Adam na sansanin.
Sai dai rahoton bai bayyana sunayen kamfanonin China da ake zargin sun shiga lamarin ba, kuma bai ce gwamnatin China ce kai tsaye ke da alhakin hakan ba.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya ce rahoton zargi ne da ba shi da tushe.
Ya ce:
“Muna matukar adawa da zato da zarge-zarge marasa tushe da ba su da wata hujja.”
Abin da Amurka ke yi wa China
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kokarin rage tasirin rahoton, wanda zai iya kara dagula alakar kasashen biyu gabanin ziyarar shugaban China, Xi Jinping, da ake shirin yi wa fadar White House ranar 24 ga Satumba.

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka
Trump ya ce China tana yi wa Amurka leken asiri, amma shi ma Amurka tana yin hakan ga China.
Ya ce:
“Kun san, idan suka ce China tana yi mana leken asiri, sai na ce kun yi gaskiya, mu ma muna yi masu haka.”
Ya kara da cewa:
“Abin da muke yi kenan. Su ma a zahiri suna yin abin da muke yi.”

Source: Getty Images
China ta bukaci a kawo hujja
Jaridar Arab News ta rahoto cewa jami’an China sun bukaci a kawo masu hujjar cewa an mika hotunan tauraron dan Adam ga Iran.
Rahoton ya ce jami’an China sun kuma ki amincewa da cewa kamfanonin kasar sun taimaka wajen bai wa Tehran hotunan sansanin sojin.
A watan Mayu, gwamnatin Amurka ta kakaba wa kamfanonin tauraron dan Adam 3 da ke China takunkumi, bisa zargin taimakawa ayyukan sojin Iran.
Batun yakin Iran da China
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai yi tunanin yakin Iran zai kare ba sai bayan zaben tsakiyar wa’adin Amurka, yana mai cewa farashin man fetur ba zai sauka ba har zuwa lokacin.
Trump ya ce shugabannin Iran za su kasa ci gaba da yakin, yana mai hasashen cewa zai kawo karshen yakin nan da nan bayan zaben.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Texas domin halartar taron farko na Jam’iyyar Republican na yakin neman zaben tsakiyar wa’adi.
Asali: Legit.ng

