Abin ba Dadi: Yan Bindiga Sun Mamayi Wasu Bayin Allah, Sun Bude Wa Motarsu Wuta
- Wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla fasinjoji tara bayan sun buɗe wa motar haya wuta a daidai titin Dungus Junction da ke Jos ta Kudu a Filato
- Rahotanni sun nuna cewa wannan mummunan lamarin ya faru ne yayin da direban motar ya tsaya domin sauke wasu fasinjoji a mahadar
- Shaidu sun ce wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga kuma an garzaya da su asibitoci domin ba su kulawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Aƙalla fasinjoji tara ne aka kashe bayan wasu ‘yan bindiga sun buɗe wa wata motar haya wuta a mahadar tituna ta Dungus Junction da ke ƙauyen Kuru, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Mazauna yankin sun shaida wa ‘yan jarida cewa lamarin ya faru ne lokacin da direban motar ya tsaya domin sauke wasu fasinjoji a mahadar, kwatsam sai ga yan bindiga.

Source: Original
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa motar bas din da ke kan hanyarta ta zuwa Jos ta jike da jini kuma harsasai sun ratsa jikinta.
Shaidu sun tabbatar da harin
Lawan Suleiman, wani maƙwabci kuma malamin ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai harin ne yayin da motar ta tsaya a mahadar.
Ya ce:
“Direban motar sunansa, Ibrahim, kuma ɗalibina ne. Uku daga cikin waɗanda aka kashe ‘yan wannan kauyen na mu ne da ke Bukuru. An kai gawarwakinsu asibiti. Amma ‘yan uwansu na shirin ɗaukar su domin binne su.”
Yadda lamarin ya faru da daddare
Kakakin ƙungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa waɗanda aka kashe fasinjoji ne da ke tafiya zuwa Jos lokacin da maharan suka buɗe wa motarsu wuta.
“Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9.40 na dare. Dukkan waɗanda aka kashe fasinjoji ne da ke tafiya zuwa Jos lokacin da ‘yan ta’addan suka buɗe wa motar wuta.

Kara karanta wannan
Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna
"Daga cikin waɗanda aka kashe akwai wani mamba na Operation Rainbow. Lamarin abin baƙin ciki ne matuƙa, kuma muna alhinin asarar rayukan,” in ji shi.
A cewarsa, wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga kuma an garzaya da su asibitoci, inda daga baya wasu suka rasu.
Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
