‘Ban Iya Addu’a ba’: Wike Ya Dogara da Matarsa domin Saka Tinubu a Addu’arsu

‘Ban Iya Addu’a ba’: Wike Ya Dogara da Matarsa domin Saka Tinubu a Addu’arsu

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana game da samun goyon baya daga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Wike ya ce ba tare da goyon bayan shugaban ƙasa ba, yana da wahala minista ya aiwatar da ayyukansa yadda ya kamata
  • Ya yabawa gwamnatin Tinubu kan goyon bayan da ta bai wa FCT, yana mai cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana yadda matarsa ke taya shi addu'a a kullum.

Nyesom Wike ya ce a kullum yana roƙon matarsa ta ci gaba da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu'a domin ya ci gaba da ba shi goyon baya.

Wike ya yi magana kan samun goyon baya daga Tinubu
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Dada Olusegun.
Source: Twitter

Wike ya yi wannan bayani ne ranar Talata yayin ƙaddamar da aikin samar da ruwan sha zuwa garin Bwari da ke ƙaramar hukumar Bwari a Abuja, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

"Ba boyewa na yi ba"; Adeyemi ya bayyana abin da yake tsoro kan badakalar PFIPC

Manyan ayyukan da Bola Tinubu ya yi

Ya ce gwamnati ta riga ta ƙaddamar da manyan ayyuka 50 a hukumance, sannan tana shirin ƙaddamar da wasu ayyuka 10 kafin watan Janairu mai zuwa.

A cewarsa, irin wannan ci gaba ya samu ne saboda cikakken goyon bayan da Shugaba Tinubu ke bai wa gwamnatin Babban Birnin Tarayya.

Wike ya ce daga gogewarsa a matsayin tsohon gwamnan Rivers da kuma minista, ya fahimci cewa ba zai yiwu minista ya yi fice ba idan ba shi da goyon bayan shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa kullum idan ya tashi daga barci, yana gaya wa matarsa, wadda ya ce ta fi shi iya yin addu'a, ta ci gaba da roƙon Allah kada Shugaba Tinubu ya daina ba su goyon baya.

Wike ya yabawa Bola Tinubu
Tsohon gwamnan Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Yabon da Tinubu ya samu daga Wike

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya bai wa Abuja dukkan tallafin da ake buƙata domin sauya fasalin babban birnin, kuma su ma ba za su ba shugaban ƙasa kunya ba.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Ya ƙara da cewa manufar gwamnati ita ce inganta rayuwar jama'a, domin idan al'umma suna farin ciki, shugabanni ma za su kasance cikin farin ciki, cewar Punch.

A cewarsa, mulki nagari shi ne wanda ke kawo sauyi mai kyau a rayuwar jama'a, kuma ya ce gwamnatin Bola Tinubu na ƙoƙarin cimma wannan buri.

Wike ya jaddada cewa gwamnatin Abuja za ta ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da cewa mazauna babban birnin tarayya suna amfana da ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa.

Wike ya ce Tinubu zabin yan Najeriya

An ji cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da sake zaben Bola Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara.

Wike ya ce Rivers ba ta da wani zaɓi illa ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 domin samar da ci gaba.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta bai wa Rivers muƙamai da ayyukan ci gaba fiye da gwamnatocin baya, yana mai kira ga jama'a su yaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.