An Kai Korafi gaban Trump kan Tikitin Muslim Muslim a Najeriya
- Wasu kungiyoyin Kirista da masu rajin kare hakki daga jihohi 36 da Abuja sun aika wa Donald Trump da Majalisar Dokokin Amurka takarda
- Kungiyoyin sun ce ci gaba da tsayawa da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2027 na iya kara tabarbarewar tsaron Kiristoci
- Kungiyar Christian Youth Alliance of Nigeria (CYAN) ta ce lakabin Country of Particular Concern (CPC) bai dakatar da kashe-kashen Kiristoci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja - Hadakar kungiyoyin Kirista da masu rajin kare hakki daga jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya Abuja sun aika wa shugaban Amurka, Donald Trump, da Majalisar Dokokin kasar takarda.
Kungiyoyin sun yi gargadin cewa ci gaba da tsayawa da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa na 2027 na iya kara tabarbarewar matsalar tsaron Kiristoci a fadin Najeriya.

Source: Twitter
Kungiyar Christian Youth Alliance of Nigeria (CYAN) ce ta mika takardar koken a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, sannan aka bai wa manema labarai kwafinta a Jos ranar Lahadi, 2 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton The Punch.
An sanya hannun Zariyi Madaki, shugaban kungiyar, da Nasiru Jagaba, sakataren kungiyar, a takardar.
Sauran wadanda suka sanya hannu sun hada da Luka Binniyat, Steven Kefas, Ier Jonathan-Ichaver, Apostle Michael Olowookere da Emmanuel Zopmal.
An nemi Amurka ta matsawa Najeriya lamba
An aika wa Trump takardar koken tare da kwafe zuwa ga Ministan Harkokin Wajen Amurka, mambobin majalisun dokokin kasar biyu da shugabannin ofisoshin jakadancin kasashen waje.
Kungiyar ta roki gwamnatin Amurka ta ci gaba da matsa wa Najeriya lamba kan abin da ta kira tabarbarewar tsaron Kiristoci.
Wani bangare na takardar ya ce:
“Muna yaba da matakin sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke da matukar damuwa ta musamman (CPC).”
Kungiyar ta ce babban amfanin wannan mataki shi ne ya karya ikirarin wasu masu yada farfaganda da ke bayyana Kiristocin da aka kashe a matsayin wadanda suka mutu sakamakon ayyukan 'yan bindiga kawai.
A cewar kungiyar, al'ummomin da abin ya shafa sun yi imanin cewa ana kai wa Kiristoci hare-hare ne saboda addini.
CYAN ta ce kisan bai tsaya ba
Sai dai kungiyar CYAN ta ce sanya Najeriya cikin jerin kasashen CPC bai dakatar da kashe-kashen ba.
Ta yi nuni da rahoton kashe akalla Kiristoci 30 a yankin Naridon da ke jihar Kaduna a makon da ya gabata.
Gargadi kan zaben 2027
Hadakar kungiyoyin ta ce wani matakin siyasa da ke faruwa a Abuja na iya kara tsananta matsalar.
A cewar takardar:
“A kimantawarmu, ci gaba da tsayawa da tikitin Musulmi da Musulmi na Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 shi ne babbar barazanar siyasa ga tsaron Kiristoci a Najeriya, musamman a Arewacin kasar.”

Source: Facebook
Kungiyar ta ce tikitin Tinubu da Kashim Shettima a zaben 2023 ya karya wata doguwar al'ada ta daidaita addinan shugaban kasa da mataimakinsa.
Takardar ta kara da cewa:

Kara karanta wannan
Ana so Atiku, Peter Obi, Kwankwaso da manyan yan adawa su goyi bayan mutum 1 a zaben 2027
“Wannan ba korafi ne na alama kawai ba, illa abu ne da ake ji a zahiri... Ya kara wa kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini da masu dauke da makamai kwarin gwiwa, duk da cewa sun dade suna aiki ba tare da fuskantar hukunci ba a al'ummomin da Kiristoci suka fi yawa.”
Gwamna Makinde ya soki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM), Seyi Makinde, ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da barin darajar naira ta riƙa sauyawa a lokaci guda sun jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng

