An Kama Matashi da Buhunan Abinci da Wasu Muhimman Kaya zai Kai wa Boko Haram
- Dakarun Operation Hadin Kai sun kama wani da ake zargi da kai wa Boko Haram da ISWAP kayan tallafi a jihar Borno
- An kwato kayan abinci, wasu muhimman kaya da wayar hannu daga hannun wanda ake zargin yayin samamen sirri da aka kai yankin Gubio
- Ana zargin mutumin ya amsa cewa yana kai wa 'yan ta'adda kayan abinci a yankin Binduldul zuwa Kareto da ke jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno –Dakarun Operation Hadin Kai sun kama wani mutum da ake zargi da kai wa Boko Haram da ISWAP kayan tallafi a wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a karamar hukumar Gubio da ke jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa wanda aka kama mai suna Modu Rayami, mai shekaru 32, ya fada hannu ne da 2.30 na rana a ranar 27 ga Yuli.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa dakarun Bataliya ta 149 da ke Gubio ne suka gudanar da aikin tare da hadin gwiwar Hybrid Forces da kuma rundunar hadin gwiwa ta (CJTF).
An kama mai taimakon Boko Haram
Rahoton ya ce an dauki matakin ne bayan samun ingantattun bayanan sirri da suka danganta wanda ake zargin da kai wa 'yan ta'adda kayan tallafi a yankin Binduldul zuwa Kareto.
An kama Rayami ne a kauyen Zowo, inda ake zargin yana dauke da kayan da aka yi imanin an tanade su ne domin isar wa 'yan ta'adda.
Kayan da aka kwato sun hada da galan biyar na man fetur, galan biyu na man ja, buhu guda-guda na gishiri, barkono da garin rogo, buhu shida na fulawa, buhu bakwai na sukari, buhu daya na lemun kwalba da kuma wayar salula.
Za a kai mai taimakon Boko Haram kotu
A cewar majiyoyin, yayin binciken farko wanda ake zargin ya amsa cewa yana kai wa mayakan Boko Haram da ISWAP fetur da kayan abinci a hanyar Binduldul zuwa Kareto.

Source: Original
A halin yanzu, ana tsare da wanda ake zargin tare da kayan da aka kwato domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
Majiyoyin soji sun ce an kammala aikin cikin nasara ba tare da wata matsala ba, kuma dakarun sun koma sansaninsu lafiya da misalin karfe 3:20 na rana.
Boko Haram ta yi rashin kunya
A baya, mun samu labarin cewa ƙungiyar Boko Haram ta bayar da wa’adin sa’o’i 72 tare da barazana kan mutane 416 da ta yi garkuwa da su a wani daji.
'Yan ta'addan sun yi barazanar rarraba su zuwa wurare daban-daban idan ba a biya bukatunta da ta zayyana wa gwamnati na tarayya ba a cikin ɗan lokaci.
Kungiyar tayar da kayan bayan Boko Haram ta yi wa gwamnati taƙama, inda ta ƙalubalance ta a aiko dakaru su zo su kwaci mutanen da ta kama idan an isa.
Asali: Legit.ng

