Manyan 'Yan Siyasa na Korafi kan Tsare El Rufa'i bayan Ya Saki Wasika

Manyan 'Yan Siyasa na Korafi kan Tsare El Rufa'i bayan Ya Saki Wasika

  • Peter Obi da Dele Momodu sun sake yin kira ga hukumomi su saki tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya kwashe watanni yana tsare
  • Obi ya ce idan akwai wani laifi da ake zargin El-Rufai da aikatawa, ya kamata a gabatar da shi gaban kotu maimakon a ci gaba da tsare shi
  • Momodu ya kuma ce bai kamata a manta da gudunmawar El-Rufai wajen samar da gwamnatin Bola Tinubu ba, yana mai sukar yadda ake tafiyar da lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da jigon ADC, Dele Momodu, sun sake yin kira da a saki tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya kasance a tsare tun watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 7 sun hada kai domin kifar da Tinubu a 2027

Obi da Momodu sun bayyana matsayarsu ne yayin da ake ci gaba da bincike da shari’o’in da suka shafi tsohon gwamnan.

Nasir El-Rufa'i na ADC
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Maganar Obi kan El-Rufai

Mai magana da yawun Obi, Idris Zekeri, ya shaida wa Punch cewa tsohon Gwamnan Anambra ya dade yana kira da a gudanar da shari’ar El-Rufai bisa tsarin doka.

Zekeri ya ce Obi ya sha yin magana kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan, yana mai cewa kotuna ne ya kamata su tabbatar da duk wani zargi da ake yi masa.

Ya ce babu wani dan Najeriya da ya kamata a ci gaba da tsare shi na dogon lokaci ba tare da an gabatar da tuhuma a kansa ba tare da mutunta hakkokinsa ba.

Zekeri ya ce:

“Peter Obi na daga cikin mutanen da suka fi yin magana tun bayan fara wannan lamari na El-Rufai.
"Ya wallafa sakonni, kuma har yanzu muna da cikakken imanin cewa idan akwai wata kara a kansa, ya kamata a tabbatar da ita maimakon a tsare shi ba bisa ka’ida ba na dogon lokaci ba tare da an magance lamarin ba.”

Kara karanta wannan

Makusantan El Rufai sun fara magana kan zargin sun yi watsi da tsohon gwamnan

Korafin Momodu kan El-Rufai

A nasa bangaren, Dele Momodu, Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Yada Labarai da Sadarwa na Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku, ya soki ci gaba da tsare El-Rufai.

Momodu ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin shirin Morning Brief na Channels Television, inda ya ce bai kamata a manta da gudunmawar tsohon gwamnan wajen samar da gwamnatin Tinubu ba.

Ya ce:

“Dukkanmu mun ga abin da ya fuskanta a hannun gwamnatin da ya taimaka wajen samarwa. Ba tare da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari da Nasir El-Rufai ba, na tabbata Shugaba Tinubu ba zai kasance kan mulki a yau ba.”
Dele Momodu a wajen taro
Jigon NDC, Dele Momodu yana wani bayani. Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Momodu ya kuma yi maraba da matakin ADC na nada El-Rufai wani matsayi a tsarin siyasar jam’iyyar duk da cewa yana tsare.

El-Rufai ya yi magana

A wani labarin, mun ruwaito cewa El-Rufai ya yi magana kan yadda wasu tsofaffin abokan tafiyarsa, abokai da ’yan uwansa suka yi shiru kan ci gaba da tsare shi.

Kara karanta wannan

Gwamna zai yi rabon tsabar kudi har Naira biliyan 6 ga talakawa

El-Rufai ya ce goyon bayan da ya bai wa mutane da wasu al’amura tsawon shekaru ya samo asali ne daga addininsa na Musulunci, tarbiyyar Arewa, da sauransu.

Ya ce halin da yake ciki a yanzu ya sa ya sake nazarin wasu daga cikin alakokinsa, amma ya jaddada cewa hakan bai kamata a dauka a matsayin hukunci ko la’akari da laifin wasu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng