Najeriya Ta Saye Sababbin Jiragen Yaki, za a Zafafa Yakar 'Yan Ta'adda

Najeriya Ta Saye Sababbin Jiragen Yaki, za a Zafafa Yakar 'Yan Ta'adda

  • Sojojin saman Najeriya (NAF) sun kammala bincike na ƙarshe na karɓar rukunin farko na jiragen yaƙi guda uku samfurin M-346 daga ƙasar Italiya
  • Wannan mataki zai taimaka sosai wajen inganta ƙwararrun ma'aikata da kuma ɗaga darajar NAF wajen kai hare-hare cikin sauri da kare ƙasa
  • Wannan na zuwa ne a zamanin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wani ɓangare na kokarin zamantar da kayan aikin soji na ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sojojin saman Najeriya sun kammala gwajin ƙarshe na karɓar rukunin farko na jiragen yaƙi guda uku samfurin M-346 FA a kamfanin Leonardo da ke Venegono, ƙasar Italiya.

Tawagar haɗin gwiwa da ta haɗa da wakilan NAF da Ma'aikatar Tsaro ta ƙasa (MOD) ce ta gudanar da aikin, inda aka cika dukkan sharuɗan kwangila kafin a tura jiragen zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An gano hanyar da aka kafa ma'aikatar bogi ta PFIPC

Sabon jirgin yakin Najeriya
Daya daga cikin jiragen yakin da Najeriya ta saya. Hoto: NAF
Source: Facebook

NAF ta wallafa a Facebook cewa shugaban Ma'aikatan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya bayyana cewa wannan nasara tana goyon bayan manufarsa ta gina sojoji masu kazar-kazar.

Sojoji sun samu jiragen yaki

Sakamakon gwajin ya tabbatar da cewa dakarun sojin saman sun sami jiragen da suka cika dukkan ƙa'idojin fasaha, kariya, da aminci na yaƙi.

Baya ga hakan, tawagar Najeriya ta tattauna da shugabannin kamfanin Leonardo kan horar da matuƙan jiragen da masana gyara, sannan da sauran tsare-tsaren tallafi na dogon lokaci.

Gwajin ya hada da duba na'urorin da suke na zamani ne da tsarin horarwa, waɗanda zasu inganta ƙwarewar ma'aikatan gida Najeriya.

Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya ƙara da cewa haɗa horon matuƙa da fasahar yaƙi da karfin M-346 yake da shi zai ƙara wa NAF damar kaddamar da hare-hare cikin sauri, tallafa wa dakarun ƙasa, da kuma kare sararin samaniyar Najeriya.

Za a yaki 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

Dakaru sun bazama farautar Dogo Gide da fitanannun yan bindiga 3 a Zamfara

NAF ta ce samar da jiragen ya nuna ƙudurin gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ƙarfafa ikon dakarun soji ta hanyar sayo ingantattun kayan aiki na zamani.

Ta ce yayin da rundunar sojin saman ke ci gaba da inganta rundunar ta, tana tsaye tsam a kan alkawarinta na kare Najeriya da tallafawa ayyukan soji na haɗin gwiwa.

Tawagar Najeriya a Italy
'Yan Najeriya da suka je karbo jirgin yaki Italy. Hoto: NAF
Source: Facebook

Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta amfani da karfin sojin sama cikin gaggawa, ƙwarewa wajen kare rayuka da dukiyoyin dukkan 'yan Najeriya.

An kama sojan Najeriya a Borno

A wani labarin, kun ji cewa dakarun Operation Hadin Kai sun samu nasarar kama wani soja da rundunar sojin Najeriya ta ke nema bisa zarginsa da laifin samar wa 'yan ta'adda kayan aiki ba bisa ƙa'ida ba.

An bayyana wanda ake zargin da soja mai lamba 23NA/84/1939 Mohammed Yusuf na ma'aikatar kayan soji ta Najeriya da ke jihar Legas.

Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a ranar 25 ga Yuli, 2026 ta hanyar wasu dakaru biyo bayan rahoton sirri da aka tattara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng