Likitan El Rufai Ya Shiga Uku da ICPC Ta Hada har da Shi cikin Shari’a a Kotu
- ICPC ta shigar da karar zargin aikata laifuffukan kawo takardun asibitin bogi a shari’ar ta da Nasir El-Rufai
- Wanda ake zargin, wato Bello Abubakar, kwararren likitan ciwon daji ne a Babban Asibitin Kasa na Abuja
- Hukumar ta ce likitan ya rubuta takarda ana neman belin El-Rufai alhali ya san bayanan da ke ciki ba gaskiya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Hukumar ICPC ta yi shigar da karar Bello Abubakar a kotu bayan tsare shi da aka yi a a sakamakon shari’ar Nasir El-Rufai.
Farfesa Bello Abubakar shi ne likitan da yake duba Nasir El-Rufai kuma kwararre ne da yake aiki a babban asibitin kasa na birnin Abuja.

Source: Twitter
ICPC tana zargin likitan Nasir El-Rufai da laifi
Premium Times ta rahoto cewa asalin zargin da ake yi wa likitan shi ne kirkirar takardun bogi domin tsohon gwamnan Kaduna ya samu beli.
Ana zargin takardar da ya gabatar wa kotu mai lamba KDH/KAD/ICPC/02/2026 da sunan takardun bayanan lafiya ba na gaskiya ba ne.
ICPC tana zargin cewa Farfesa Bello Abubakar ya nemi ya yaudari hukuma, a ba Malam El-Rufai beli da sunan yana fam da rashin lafiya.
Farfesan kwararre ne a kan cututtukan daji a babban asibitin da ke babban birnin Abuja, an dauke shi na gajeren lokaci ne bayan ya yi ritaya.
Likitan ya mika wa kotu wannan takarda a ranar 10 ga watan Yuni 2026 a matsayin hujjar da ke dauke da bayanan rashin lafiyar El-Rufai.
Tuhume-tuhumen da aka yi wa likitan El-Rufai
Tuhumar farko da ake yi wa Farfesa Abubakar ita ce bada bayanan karya da nufin a yaudari jami’in gwamnati wanda ya saba dokar ICPC.
Laifi na biyu da ake zargin ya aikata shi ne yunkuarin amfani da matsayinsa ta hanyar da ba ta dace be wajen gabatar da rahoto na bogi.

Source: Twitter
Rahoton ya ce ana zargin farfesan da hada-kai da wani Aliyu Bala domin a kirkiri bayani na karya, wannan ya ci karo da dokar final-kwad.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Kotu ta yi hukunci kan takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban ƙasa na 2027
A karshe lauyoyin ICPC suna tuhumar shi da kawo takardar karya, ya nuna tamkar cewa ta fito ne daga babban asibitin na Abuja.
Hukumar ICPC ta ce likitan ya san ba daga asibitin takardar da ta fito ba, amma ya gabatar wa kotu.
Shugaban asibitin Abuja zai kare ICPC a kotu
Shugaban asibitin na Abuja, Raji Mahmud ake sa ran zai bada shaida a kotu domin ya karfafa zargin da ICPC ta ke yi wa babban likitan.
Dakta Raji Mahmud zai yi wa kotu bayanin yadda Farfesa Abubakar ya kawo wannan takarda ba tare da an yi wa El-Rufai wasu gwaji ba.
Takardun karar da aka gani sun nuna shugaban asibitin zai fada wa alkali cewa ba a bi ka’ida wajen samun wannan takardar bayanan ciwo ba.
Matar El-Rufai ta yi kira ga duniya
An ji cewa Asia Ahmad El-Rufai, matar tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ta wallafa rubutu a wata jarida ta duniya don yin tir da tsare mijinta.
Mai dakinsa ta fadi halin da Nasir El-Rufai ke ciki a yanzu, ta yi kira ga ƙasashen waje su tsoma baki kan tsare mijinsu da aka yi tun Fubrairu 2026.
Asia ta bayyana cewa tsare shi da aka yi ba tare da beli ba ya saba wa ka'idojin adalci, kuma ta yi kira ga abokan hulɗar ƙasa da ƙasa su kare shi.
Asali: Legit.ng
