Malamin Addini Ya Garzaya Kotu Neman a Ba Shi Tikitin ADC na Takarar Gwamnan Kano
- Sheikh Ibrahim Khalil ya roƙi Kotun Tarayya ta umarci ADC ta sauya sunan Ibrahim Little da aka miƙa wa INEC da nasa
- Ibrahim Khalil, wanda ke jagorantar Majalisar Malamai ta Kano, ya ce shi ne wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na ADC kafin sauya shugabancin jam’iyyar
- ADC ta miƙa sunan Ibrahim Little a matsayin ɗan takararta na gwamnan Kano, bayan da aka rushe shugabancin jam’iyyar na jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya shigar da ƙara a Kotun Tarayya kan jam'iyyarsa ta ADC.
Sheikh Ibrahim Khalil yana neman a umarci jam’iyyar ADC ta cire sunan Ibrahim Ali Amin, wanda aka fi sani da Ibrahim Little, daga jerin sunayen da ta miƙa wa INEC a matsayin ɗan takararta na gwamnan Kano a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Pantami na murnar samun tikitin PDP, abokin hamayyarsa ya sha alwashin jawo masa matsala

Source: Facebook
Sheikh Khalil ya nemi a sauya sunan ɗan takarar ADC
Sheikh Khalil na neman a maye gurbin sunan Ibrahim Little da nasa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ibrahim Khalil, wanda shi ne shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ya tsaya takarar neman tikitin ADC a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.
ADC ta taɓa ayyana nasarar Khalil
A cewar bayanan ƙarar, ADC ƙarƙashin tsohon shugaban jam’iyyar na Kano, Musa Ungogo, ta ayyana Sheikh Khalil a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani.
Sai dai bayan rushe shugabancin jam’iyyar na jihar, ADC ta miƙa sunan Ibrahim Ali Amin (Little) ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na gwamna.
Ibrahim Little ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin makusantan siyasar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar.
Lauyoyin sun tabbatar da karɓar takardun kotu
Lauyan Sheikh Khalil, AA Abubakar, ya shaida wa kotun cewa an kai takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara.
Lauyan Ibrahim Little, wanda shi ne wanda ake ƙara na biyu a shari’ar, ya kuma tabbatar wa kotun cewa an miƙa musu takardun kamar yadda lauyan Sheikh Khalil ya bayyana.
ADC ta zaɓi Ibrahim Little a watan Yuli
A watan Yuli, ADC ta zaɓi Alhaji Ibrahim Ali Amin, wanda aka fi sani da Ibrahim “Little”, a matsayin ɗan takararta na gwamnan Kano a zaɓen 2027. Matakin ya kawo ƙarshen makonni da aka shafe ana takaddama da rashin tabbas kan wanda zai riƙe tikitin jam’iyyar a Kano, jihar da ke da yawan jama’a a Najeriya.
Mukaddashin shugaban ADC na Kano, Dr Umar Bala Kwalwa, ya miƙa wa Ibrahim Little fom ɗin takarar gwamna na INEC, EC-13B a wancan lokacin.
Miƙa fom ɗin ya zama tabbacin cewa jam’iyyar ta amince da Ibrahim Little a matsayin ɗan takararta na gwamnan Kano a zaɓen 2027.

Source: Facebook
''Yan takarar ADC sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan takarar kujerun Majalisar Dokokin Jiha na jam’iyyar ADC daga jihohin Zamfara, Plateau, Taraba da Jigawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Waɗanda suka sauya sheka sun kuma bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

