An Kama Matasa 2 kan Kashe Uwa Mai 'Ya'ya 5 yayin Satar Waya a Gombe

An Kama Matasa 2 kan Kashe Uwa Mai 'Ya'ya 5 yayin Satar Waya a Gombe

  • Rundunar ’Yan Sandan Gombe ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu wajen fashi da makami da kashe matar wani jami’in ɗan sanda
  • An kashe matar ne bayan wasu da ake zargi da fashi sun kai hari gidansu da ke unguwar Wuro Shi'e a jihar Gombe
  • ’Yan sandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a laifin yayin binciken farko, inda aka kwato wata wuka mai kaifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da kama mutum biyu da ake zargi da hannu wajen fashi da makami da kashe matar wani jami’in ɗan sanda a unguwar Wuro Shi'e.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:35 na asuba ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu mutane ɗauke da adduna da wuƙaƙe suka kutsa gidan Inspector Salisu Waziri.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rutsa mutane a zungureren rami, an rasa rayuka da dama

Aisha Ibrahim da aka kashe
Matar auren da aka kashe a Gombe. Hoto: Sarkin Adon Pantami
Source: Facebook

Jami’in yana aiki ne da rundunar Safer Highway Patrol, yayin da matar tasa, Aishatu Salisu, ke gidan a lokacin da waɗanda ake zargin suka kai harin.

Rundunar ta ce mutanen sun yi ƙoƙarin ƙwace wayar salular matar, amma ta ɗaga murya domin neman agaji.

A cewar ’yan sandan, ɗaya daga cikin maharan ya sare ta da adduna kafin su tsere, inda suka bar wayar a wurin.

’Yan sanda sun kama mutum 2

Bayan samun rahoton, jami’an sintiri na sashen ’yan sanda na Pantami sun garzaya wurin tare da kai Aishatu zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe.

Sai dai asibitin ya tabbatar da cewa ta rasu sakamakon raunin da ta samu.

Bayan faruwar lamarin, rundunar ta fara bincike tare da ƙara kaimi wajen gano mutanen da ke da hannu a harin.

A sakamakon binciken, an kama Muhammad Bashir Sale, mai shekaru 20, wanda aka fi sani da “Full”, da Musa Sale Ahmad, mai shekaru 18, wanda aka fi sani da “Abba”.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama matar aure kan yanayin yadda saurayinta ya mutu a ɗakin Otal

Dukkan mutanen biyun mazauna Gombe ne. Rundunar ta ce a yayin binciken farko, waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a laifin.

Haka kuma, an kwato wata wuka mai kaifi da aka ajiye a matsayin shaida.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Za a zurfafa bincike

Leadership ta wallafa cewa a halin yanzu, an miƙa binciken lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar Gombe, wato CID.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin sirri domin tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu ya fuskanci hukunci.

Rundunar ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ma'aikaci ya yi sata a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da aikin Abdulkadir B. Aliyu, wani babban jami’in kashe gobara na jihar, kan zargin sata da rashin ɗa’a.

Aliyu, wanda ke aiki a sashen kashe gobara na Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri, an same shi da laifin satar takalman wasu mutane yayin gudanar da sallah a Babban Masallacin Sakatariyar Abubakar Umar da ke Bauchi.

Hukumar ta ce ta yanke shawarar dakatar da aikinsa ne bayan ta bi dukkan matakan ladabtarwa da dokokin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi suka tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng