An Fallasa Kuskuren Gwamnatin Tarayya da Ya Karfafa Ayyukan Boko Haram a Arewa

An Fallasa Kuskuren Gwamnatin Tarayya da Ya Karfafa Ayyukan Boko Haram a Arewa

  • Tsohon IGP Mike Okiro ya ce rushe rundunar ATS da ya kafa ne ya ba Boko Haram damar samun ƙarfi da bazuwa a Najeriya
  • Okiro ya bayyana cewa ya horas da jami'an ATS a ƙasashen waje tare da kafa cibiyar horaswa a Ribas domin yaƙi da ta'addanci
  • Ya yi zargin cewa rashin goyon bayan gwamnati da dakatar da shirin ne ya raunana matakan dakile Boko Haram tun daga farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Tsohon Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya (IGP), Sir Mike Mbama Okiro, ya bayyana cewa dakatar da rundunar yaƙi da ta'addanci (ATS) da ya kafa a lokacin mulkinsa ya taimaka wajen bai wa ƙungiyar Boko Haram damar samun ƙarfi a ƙasar.

Sir Mike Mbama Okiro dai ya ya jagoranci rundunar 'yan sandan Najeriya daga ranar 1 ga Yunin 2007 zuwa 24 ga Yulin 2009.

Kara karanta wannan

Jigon ADC: 'Hari kan mahaifar mataimakin gwamna ya nuna ba mafaka a Sokoto'

Tsohon IGP, Mike Okiro ya fadi yadda Boko Haram ta kara karfi a Najeriya
Sir Mike Mbama Okiro, tsohon sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya. Hoto: @david_azuh
Source: Twitter

Yadda aka kafa rundunar ATS

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Sunday Sun, inda ya ce wasu matakan da aka ɗauka bayan ya bar ofis sun raunana tsarin tsaron da aka gina domin dakile barazanar ta'addanci.

Tsohon IGP ya ce cikin watanni kaɗan bayan hawansa mulki ya kafa rundunar ATS, sannan ya tura jami'anta zuwa Isra'ila, Masar, Sudan da Afirka ta Kudu domin samun horo kan dabarun yaƙi da ta'addanci.

Ya ƙara da cewa domin rage kuɗin tura jami'ai ƙasashen waje, ya kafa cibiyar horas da jami'an ATS a jihar Ribas.

Sai dai ya ce shirin ya fuskanci suka daga wasu kafafen yaɗa labarai da suka zarge shi da kafa rundunar ne domin kai hari ga wata addini, abin da ya sa ya fito ya yi wa jama'a bayani.

Ya ce gwamnati ta dakatar da tallafin ATS

A cewar Okiro, cece-kuce kan rundunar ya sa gwamnati ta ƙi amincewa da kasafin kuɗin da aka ware domin sayen motocin aiki da kayan sadarwa ga ATS.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Ya kuma ce bayan ya tura jami'an rundunar zuwa Legas, Fatakwal, Kano da Maiduguri, wasu gwamnoni sun buƙaci a janye su daga jihohinsu, kuma ya bi umarnin.

Tsohon shugaban 'yan sandan ya bayyana cewa tun kafin ya yi ritaya yana bibiyar marigayi shugaban Boko Haram, Mohammed Yusuf, yana mai cewa ya taɓa kama shi sau da dama.

Tsohon IGP ya ce an an bar rundunar ATS da yanzu Boko Haram ba ta yi karfi ba
Sir Mike Mbama Okiro, tsohon sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya.
Source: Facebook

"Da Boko Haram ba ta yi ƙarfi ba" - Okiro

Okiro ya jaddada cewa da gwamnati ta ci gaba da goyon bayan rundunar ATS tare da samar mata da kayan aiki, da Boko Haram ba za ta bazu zuwa sassa daban-daban na Najeriya ba.

Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda cibiyar horas da jami'an ATS da ya kafa a jihar Ribas ta daina aiki, yana mai cewa Najeriya na buƙatar koyo daga irin waɗannan kura-kurai domin ƙarfafa tsaro da dakile barazanar ta'addanci a nan gaba.

An kashe mai daukar bidiyon Boko Haram

A wani labari, mun ruwaito cewa, Boko Haram ta tabbatar da mutuwar babban mai ɗaukar bidiyonta, Abu Salim al-Barnawi, a wani harin sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

An ayyana neman wani sojan Najeriya ruwa a jallo, an saki hotuna da bayanansa

Rundunar Operation Hadin Kai ta ce an kashe wasu manyan mayaƙa tare da Abu Salim, yayin da aka kwato kyamara da sauran kayan aiki.

Sojoji sun ce mutuwar Abu Salim ta raunana ƙarfin yaɗa farfagandar Boko Haram da kuma ƙoƙarin ƙungiyar na jan hankalin sababbin mayaƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com