'Yan Ta'adda Sun Bani, Shugaba Tinubu Ya Fadada Rundunar Sojojin Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙara rukunonin rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya daga guda takwas din da ake da su
- Hakazalika, gwamnatin tarayya za ta ɗauki sababbin jami'an sojoji 28,000 domin ƙarfafa tsaron ƙasa
- Za a aiwatar da sabon tsarin a matakai biyu, wanda za a kammala gaba ɗaya kafin ƙarshen shekarar 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da faɗaɗa rundunar sojojin ƙasan Najeriya daga rukunoni takwas zuwa 12.
Hakazalika, shugaban kasar ya amince da daukar sababbin jami'an sojoji 28,000 domin samar da tsaro a kasa.

Source: Facebook
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026 a shafin X.
Ya ce wannan mataki wata babbar nasara ce wajen ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya da kuma inganta yadda rundunar sojojin ƙasa ke gudanar da ayyukanta.
Tinubu zai ƙarfafa rundunar sojoji
Onanuga ya ce wannan amincewa na nuna ƙudirin Shugaba Tinubu na samar wa rundunar sojoji kayan aiki da damar da za su taimaka mata wajen tunkarar sauye-sauyen barazanar tsaro da ƙarfafa ƙarfin kare ƙasar.
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya ginu ne kan ci gaba da zuba jari da gwamnatin Tinubu ke yi a fannin tsaro.
A cewarsa, hakan ya haɗa da sayen muhimman kayan aikin soja, inganta jin daɗin jami'an soja da kuma ƙarfafa shirye-shiryen gudanar da ayyukan tsaro da sabunta rundunar.
Rukunonin rundunar sojoji da yankunan aikinsu
Sabon tsarin rukunonin rundunar sojojin ƙasan Najeriya zai kasance kamar haka:
1. Runduna ta 1 – Kaduna (Jihohin Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa)
2. Runduna ta 2 – Ibadan (Jihohin Oyo, Osun, Ekiti da Ondo)
3. Runduna ta 3 – Jos (Jihohin Plateau, Bauchi da Gombe)
4. Runduna ta 5 – Makurdi (Jihohin Benue, Nasarawa da Kogi)
5. Runduna ta 6 – Port Harcourt (Jihohin Rivers, Akwa Ibom da Cross River)
6. Runduna ta 7 – Maiduguri (Jihohin Borno da Yobe)
7. Runduna ta 8 – Sokoto (Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara)
8. Runduna ta 9 – Ilorin (Jihohin Kwara da Niger)
9. Runduna ta 10 – Jalingo (Jihohin Taraba da Adamawa)
10. Runduna ta 81 – Legas (Jihohin Legas da Ogun)
11. Runduna ta 82 – Enugu (Jihohin Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi da Imo)
12. Runduna ta 83 – Benin City (Jihohin Edo, Delta da Bayelsa)
Amfanin sababbin rundunonin
Sanarwar ta ce kafa sababbin rundunoni a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin zai inganta jagoranci da sa ido kan ayyukan soja.
Haka kuma, zai ba da damar rarraba yanke shawarar gudanar da ayyukan tsaro zuwa yankuna daban-daban, ƙarfafa tsaron kan iyakoki, kare muhimman cibiyoyin ƙasa da kuma inganta yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaro na cikin gida.
Bugu da ƙari, sabon tsarin zai taimaka wajen saurin mayar da martanin soji ga duk wata barazana da ka iya tasowa a sassan ƙasar.

Source: Twitter
Yadda za a aiwatar da shirin
A cewar sanarwar, za a aiwatar da sabon tsarin fadada rundunar sojojin kasan a matakai biyu.
Mataki na farko ya haɗa da kafa rundunoni na 5, 9 da 10 tare da sake fasalin rundunonin da ake da su, kuma ana sa ran za a kammala shi kafin watan Satumban 2026.
Mataki na biyu kuwa zai haɗa da kafa Runduna ta 83 da kuma ci gaba da sake fasalin sauran rundunoni, wanda ake sa ran za a kammala kafin watan Disamban 2026.
Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka sama da mayaƙan kungiyar 'yan ta'addan ISWAP 20.
An hallaka mayakan ne a wani harin jirgi mara matuƙi da bangarrn rundunar sojojin sama ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta kai a Kila Bariya, a yankin Kudancin Tafkin Chadi.
Asali: Legit.ng


