Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya

Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya

- Kakakin rundunar sojin Najeriya, manjo janar John Enenche, ya ce saura kiris sojoji su gama da 'yan bindiga

- Enenche ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Abuja, inda yace kowa ya sha kuruminsa

- Ya bayar da misali da yadda ta'addanci ya lafa a jihar Katsina da Zamfara, saboda 'yan ta'addan sun kusa karewa

A ranar Alhamis rundunar sojin Najeriya tace tana samun nasarori, kuma tana dab da kawo karshen ta'addanci da rashin tsaro a kasar nan.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wani taro a Abuja. Enenche ya bayar da misalin yadda suka ci karfin ta'addanci a jihar Zamfara da Katsina.

A wata takarda ta ranar Litinin, Enenche ya sanar da yadda rundunar Operation Hadarin Daji ta kashe a kalla 'yan bindiga 35 a jihar Zamfara a karon batta guda biyu da suka yi.

KU KARANTA: Bauchi: An daurawa matashi aure da gawar budurwarsa a kan sadaki N2000

Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya
Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Sun fita farautar 'yan bindigan ne a ranar Lahadi, kamar yadda kakakin yace. Sun samu nasarar kwatar shanu 24 da kuma tumaki da dama daga hannun 'yan ta'addan.

Ya kuma bayyana yadda suka samu nasarar damkar 'yan ta'adda guda biyu a jihar Katsina, Channels Tv ta wallafa.

Har ila yau, Enenche ya bukaci jama'a su dinga sanar da sojoji labarai masu amfani da zasu taimaka wurin kama 'yan ta'addan.

KU KARANTA: Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a jiya ya ce majalisar tarayya bata da dalilin da zai sa ta yaki shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda tana son farantawa wasu rai a kasar nan.

Lawan ya sanar da hakan ne a yayin da ya karbar wakilai daga jihar Adamawa wadanda suka ziyarcesa domin nuna jin dadi ga majalisar tarayya a kan yadda ta sauya jami'ar Modibbo Adama da ke Yola.

Wakilan sun samu jagorancin Sanata Aishatu dahiru Ahmed da kuma shugaban jami'ar, farfesa Abdullahi Lima Tukur, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel