An Zo wajen: An Fara Shirin Daina kai Shanu daga Arewa zuwa Kudu

An Zo wajen: An Fara Shirin Daina kai Shanu daga Arewa zuwa Kudu

  • Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin samar da kusan guraben aikin yi 10,000 daga kowanne katafaren gidan yanka shanu da zai iya sarrafa shanu 500 a rana
  • Ministan Kiwo, Alhaji Idi Maiha, ya ce hakan na daga cikin matakan sauya tsarin kiwo, musamman daina jigilar dabbobi masu rai daga Arewa zuwa Kudu
  • Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi su haɗa hannu da kamfanoni masu zaman kansu wajen kafa gidajen yanka na zamani domin samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kafa gidajen yanka shanu na zamani a faɗin ƙasar na daga cikin shirinta na bunƙasa harkar kiwo da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ministan Ma'aikatar Kiwo, Alhaji Idi Maiha, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umaru Bago na Jihar Neja yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu domin duba ayyukan L-PRES a Minna ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Shanu a cikin mota
Yadda ake saka shanu a mota. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun jigilar shanu zuwa Kudu

Punch ta wallafa cewa Maiha ya ce gwamnati na sa ran wajen sarrafa shanu 500 a rana zai iya samar da kusan guraben aiki 10,000 idan aka kafa shi ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ya ce irin waɗannan wurare za su samar da damarmaki ga matasa a fannonin kiwon shanu, noman ciyawar dabbobi, samar da abinci, kiwon lafiya da sufuri.

Ministan ya ce hakan zai taimaka wajen sauya harkar daga jigilar dabbobi masu rai zuwa jigilar naman da aka sarrafa cikin yanayin sanyi.

Ya ce jigilar dabbobi daga Arewa zuwa Kudu na haifar da raguwar nauyin dabbobi, haɗurran abubuwan hawa, ɓarna da kuma rashin samun cikakkiyar darajar da za a iya samu daga dabbobin.

Za a inganta harkokin kiwo

Maiha ya ce ma’aikatarsa ta ware samar da abinci da ciyawar dabbobi, inganta jinsin dabbobi da kula da lafiyar dabbobi a matsayin manyan abubuwa uku da take bai wa fifiko.

Kara karanta wannan

Akwai alheri: An buɗe shirin da ake buƙatar matasa 'yan shekaru 15 zuwa 35 su cike a Najeriya

Ya kuma ce za a yi aiki tare da gwamnatocin jihohi wajen kafa cibiyoyin raya kiwo da za su ba makiyaya damar zama tare da bunkasa sana’o’in da suka shafi kiwo.

Ministan ya bayyana cewa kiwo na yawo ba al’ada ba ce, sai dai hanyar rayuwa ce da makiyaya ke amfani da ita wajen motsa dabbobinsu daga wuraren da abinci ya yi ƙaranci zuwa wuraren da yake da yawa.

Wasu shanu a wajen kiwo
Wasu shanu a wajen kiwo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce inganta kiwo zai taimaka wajen ƙara samar da madara a Najeriya, yana mai cewa ƙasar na kashe kusan dala biliyan 1.5 duk shekara wajen shigo da kayayyakin madara daga ƙasashen waje duk da cewa tana da kusan shanu miliyan 55.

Neja za ta bunkasa harkar kiwo

Rahoton MSME Africa ya nuna cewa Gwamna Umaru Bago ya ce Jihar Neja za ta magance ƙarancin ciyawar dabbobi ta hanyar ƙara noman abincin dabbobi.

Bago ya ce jihar ta samu dala miliyan 100 daga Bankin Exim na Saudiyya, inda aka fara ware dala miliyan 10 domin ayyukan ban ruwa da za su tallafa wa noman ciyawar dabbobi.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Ya ce shirin zai samar da ruwa, abinci, wuraren kiwo da kuma ayyukan kula da lafiyar dabbobi, tare da samar da abubuwan da za su ƙarfafa makiyaya su zauna su shiga tsarin kiwo na zamani.

INEC za ta dauki aiki

A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta buɗe shafinta na neman ma’aikatan wucin gadi da za su taimaka wajen gudanar da babban zaɓen 2027.

Ana gudanar da neman aikin ne ta tsarin ɗaukar ma’aikatan hukumar, kuma an buɗe damar ga ’yan Najeriya da suka cika sharudan shiga aikin gudanar da zaɓe a faɗin ƙasar.

INEC ta ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har zuwa tsakar daren 18 ga Nuwamba 2026, inda ta buƙaci masu sha’awar aikin su kammala aikace-aikacensu kafin wa’adin ya cika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng