Jigon ADC: 'Hari kan Mahaifar Mataimakin Gwamna Ya Nuna Ba Mafaka a Sokoto'
- Ɗan takarar gwamnan ADC a jihar Sokoto ya zargi gwamnatin tarayya da ta Ahmed Aliyu da gaza shawo kan matsalar tsaro har ya na kara fadada
- Ya ce sace mutane sama da 50 a Garin Idi ya nuna babu wani yanki da ke da kariya daga hare-hare da ta'addancin yan bindida da ke damun yankin
- 'Dan takarar gwamnan ya bukaci a ƙarfafa tsaro, kama masu laifi tare da tallafa wa al'ummomin da abin ya shafa wanda tuni aka raba su da yan uwansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na jam'iyyar ADC, Hon. Mannir Muhammad Dan'iya, ya dora alhakin tabarbarewar tsaro kan gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Sokoto.
Ya bayyana haka ne bayan rahotannin sace fiye da mutum 50 a Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar, Idris Mohammed Gobir.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito dan takarar gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, 2026.
Dan takarar ADC ya soki gwamnatin Sokoto
Dan'iya ya ce wannan hari ya nuna yadda matsalar tsaro ta yi kamari har yankunan da ke da alaƙa da manyan jami'an gwamnati ba su tsira daga hare-haren 'yan bindiga ba.
Ya ce hare-haren da ake kai wa, sace-sacen mutane da kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a sassan jihar sun nuna gazawar gwamnati wajen cika nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Dan'iya ya ce:
"Rahoton sace fiye da mazauna Garin Idi 50 ya nuna cewa rashin tsaro ya bazu matuƙa har yankunan da ke da alaƙa da manyan jami'an gwamnati ba su da kariya daga ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifukan makami."
Gwamnati ta gaza cika alkawari - Dan takarar ADC
Ya kuma yi nuni da sashe na 14(2)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, inda ya ce tsaro da jin daɗin jama'a su ne babban manufar gwamnati, inda ya kara da cewa babu wata al'umma da za ta samu ci gaba mai ma'ana idan mutanenta na rayuwa cikin tsoro.
Dan'iya ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa mazauna yankin sun tattauna kai tsaye da 'yan bindiga tare da tara kuɗi domin kuɓutar da matan da aka sace, tsofaffi da almajirai.

Source: Twitter
Ya ce idan wannan rahoto gaskiya ne, yana nuna irin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da al'ummomin da abin ya shafa suka shiga, tare da nuna buƙatar ƙarin jami'an tsaro, inganta tattara bayanan sirri da kuma gaggauta kai ɗauki a yankunan da ke cikin haɗari.
Dan'iyan ya ce sabon harin ya kamata ya sa gwamnati ta sake duba dabarun tsaronta tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da al'ummomi domin dakile tashe-tashen hankula.
An sace mutane 50 a jihar Sokoto
A baya, mun kawo labarin cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan Sokoto, inda suka sace fiye da mutum 50 aka yi garkuwa da su.
Mazauna garin sun ce maharan sun karɓi N600,000 kafin su saki mutanen, sannan suka umarci al'umma su biya karin N1m cikin kwana biyu, lamarin da ya jefa rayuwar jama'a a cikin mawuyacin hali.
Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta ce ba ta samu wani rahoto kan harin ba, yayin da mazauna yankin ke neman agajin gwamnati, a dai-dai lokacin da jami'an tsaro ke cewa su na aikin tabbatar da tsaro a Najeriya.
Asali: Legit.ng


