PFIPC: Atiku Ya Ba Majalisa Mafita bayan CBN da Akanta Janar Sun Yi Baki 2
- 'Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya bukaci Majalisar Tarayya ta gayyaci gwamnan CBN da Akanta Janar kan asusun PFIPC
- Ya ce bayanan da hukumomin biyu suka bayar sun saba wa juna, lamarin da ya jefa gwamnati a cikin matsala da kuma jama'ar gari a cikin kokwanto
- Dan takarar shugaban kasa na NDC ya kuma bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zaman kansa a kan wannan matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Atiku Abubakar, ya bukaci Majalisar Tarayya ta gayyaci gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Akanta Janar na Tarayya.
Ya ce akwai bukatar a gayyaci bangarorin biyu domin su yi bayani kan sabanin da ke tattare da asusun hukumar bogi ta PFIPC da ake ta magana a kai.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito wannan na bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Laraba 22 ga watan Yuli, 2026.
Atiku ya magantu kan CBN
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Atiku ya ce sabanin bayanan da CBN da Ofishin Akanta Janar suka bayar ya jefa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin babbar matsalar amincewar jama'a.
Ya ce shaidar da CBN ya bayar a gaban Majalisar Wakilai ta saba da bayanin da Ofishin Akanta Janar ya yi tun farko kan yadda aka bude asusun PFIPC.
Alhaji Atiku Aabubakar ya yi zargin cewa wannan rashin daidaito na iya nuna akwai kokarin boye gaskiyar abin da ya faru a batun kafa hukumar PFIPC.
Ya ce:
"A nan ne ake ganin an fara kokarin rufe gaskiya. Wata hukuma ta ce ba ta ba da izinin bude asusun PFIPC ba, har ma ta yi zargin an yi jabun takardu."
Ya kara da cewa:
"Sai kuma wata hukuma ta shaida wa wakilan jama'a cewa an bude asusun ne bisa umarnin Akanta Janar bayan an bi duk ka'idoji. Wadannan bayanai biyu ba za su iya zama gaskiya lokaci guda ba."
Bukatar Atiku ga Tinubu
Atiku ya ce sabanin bayanan ya nuna gwamnatin tarayya ta fada cikin abin da ya kira "tarkon yaudara", yana mai cewa bai kamata shugaba ba zai ci gaba da kallon lamarin daga gefe ba.
Ya ce:
"Idan manyan hukumomin kula da harkokin kudi biyu na kasar nan suna musanta juna a bainar jama'a kan ma'amala guda, hakan na nuna akwai babbar matsalar gaskiya da amincewa."

Source: Twitter
A cewarsa:
"Dole ne shugaba Tinubu ya amsa tambaya mai sauki: Wane bayani ya yarda da shi, na Akanta Janar ko na Babban Bankin Najeriya? Idan bai yarda da ko daya ba, me ya sa har yanzu bai dauki mataki ba?"
Atiku na son Tinubu ya yi murabus
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta boye Naira tiriliyan 12.8 a kasafin 2026, yana zargin hakan barazana ce ga gaskiya da rikon amana da ake nema a wajen shugaba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin Tinubu ta bayyana dalla-dalla yadda za a kashe kudaden Service-Wide Vote da aka ware domin tabbatar da abin da aka shirya za a yi da su.
Atiku ya bukaci Majalisar Tarayya ta binciki dukkan kudaden Service-Wide Vote domin tabbatar da gaskiya da kare dukiyar al’umma daga almubazzaranci tare da zargin ana son a yi amfani da su a fakaice.
Asali: Legit.ng


