Sokoto: Dan Majalisar Tarayya Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamna a ADC
- Jam'iyyar ADC ta ayyana dan majalisar tarayya a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna a Sokoto
- An zabi Hon. Bello Isah Ambarura a matsayin mataimakin dan takarar gwamnan Sokoto na zaben shekarar 2027
- Jam'iyyar ta ce nadin ya biyo bayan tuntuba, tare da bin tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya domin samar da ingantaccen jagoranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Jam'iyyar ADC a Sokoto ta sanar da nada dan Majalisar Wakilai a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna.
An nada Ɗan majalisar mai wakiltar mazabar tarayya ta Illela/Gwadabawa, Hon. Bello Isah Ambarura saboda jajircewarsa.

Source: Facebook
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na ADC a Sokoto, Hon. Lamir Aminu, ya fitar, cewar Tribune.
Hanyar da aka bi kafin zaben Ambarura
Sanarwar ta ce Ambarura zai yi takara tare da dan takarar gwamna, Hon. Manir Muhammad Dan-Iya domin fafatawa a zaben shekarar 2027.
A cewar Aminu, an yi nadin ne bayan gudanar da tuntuba mai fadi tsakanin shugabannin jam'iyyar, tare da bin tanadin sashe na 187(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya ce matakin ya nuna kudurin jam'iyyar na gabatar da tikitin da ya kunshi mutane masu kwarewa, nagarta da kuma mayar da hankali kan bukatun al'ummar Sokoto.
A cikin sanarwar, Aminu ya ce an yi nadin ne bayan nazari mai zurfi kan halayen da ake bukata domin gina tawagar shugabanci mai karfi, kwarewa da kuma kishin jama'a.

Source: Facebook
Yabon da Ambarura ya samu daga ADC
Ya bayyana Ambarura a matsayin gogaggen jami'in gwamnati wanda ya fara aiki a ma'aikatan gwamnatin Sokoto har ya zama Babban Sakatare na dindindin, sannan ya taba zama Kwamishinan Kasuwanci da Masana'antu.
Aminu ya kara da cewa Ambarura ya zama dan Majalisar Dokokin Sokoto a shekarar 2019, inda ya yi aiki a matsayin Jagoran Masu Rinjaye har zuwa 2023, kafin daga bisani ya lashe kujerar Majalisar Wakilai, cewar Punch.
Jam'iyyar ADC ta ce kwarewar Ambarura a harkokin gudanarwa da majalisa za ta karfafa jagorancin Manir Muhammad Dan-Iya, tare da neman mambobi, magoya baya da al'ummar Sokoto su mara wa tikitin Dan-Iya da Ambarura baya a zaben 2027.
Ana hasashen za a kai ruwa rana tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kuma ADC da ta tara manyan ƴan siyasa yayin da ake shirin zaben shekarar 2027.
ADC ta nemo hanyar kayar da Tinubu
Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar ADC ta bayyana kwarin gwiwar cewa tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi zai kayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce wahalar rayuwa, yunwa da rashin tsaro za su sa 'yan Najeriya su nemi sauyi a 2027.
ADC ta kuma yi zargin cewa APC na shirin yin magudin zaɓe, amma ta ce al'umma za su kasance cikin shiri domin hana duk wata murdiya.
Asali: Legit.ng

