'Yabon Trump Ya Nuna Aikinmu Ya na Kyau': Fadar Shugaban Kasa
- Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yabon da Donald Trump ya yi wa Bola Tinubu ya samo asali ne daga haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka
- Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce haɗin gwiwar ya taimaka wajen murƙushe hare-haren ta'addanci tare da musayar bayanan sirri
- Kalamansa sun biyo bayan wata wasika da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya aiko wa da Bola Ahmed Tinubu ya na yabonsa kan yakar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa wasiƙar yabo da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya aikawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da kokarinsu.
Ya kara da cewa wannan 'yar manuniya ce ga irin ci gaban da aka samu a haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka wajen kakkabe ayyukan ta'addanci.

Source: Getty Images
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana haka yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.
Fadar shugaban kasa magantu kan Trump
Nigerian Tribune ta wallafa cewa a cewarsa, wasiƙar ba wai gaisuwar diflomasiyya ba ce kawai, illa dai ta amince da irin nasarorin da aka samu ta hanyar musayar bayanan sirri, atisayen soji da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Bwala ya ce:
"Wannan yabo ne ga sakamakon haɗin gwiwa da ya kai wani mataki mai zurfi kuma abin yabawa. An kashe mutum na biyu mafi girma a ISIS a duniya a Najeriya ta hanyar aikin haɗin gwiwa."
Ya ƙara da cewa:
"Mun dakile hare-harensu saboda wannan haɗin gwiwa. Muna musayar bayanan sirri, muna horas da jami'ai a gida, sannan muna gudanar da hare-haren haɗin gwiwa."
Gwamnati na karfafa ayyukan tsaro - Bwala
Bwala ya ce gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan inganta rayuwar 'yan Najeriya ta fuskar tattalin arziki, ilimi da tsaro, maimakon mayar da martani ga suka daga jam'iyyun adawa.
Ya ce duk da cewa har yanzu ana fuskantar hare-hare a wasu yankuna, akwai ci gaba mai ma'ana a yaƙi da ta'addanci da dawo da zaman lafiya.

Source: Facebook
A cewarsa:
"Abin da ake aunawa shi ne ci gaban da mu ke samu, wanda ya sa shugaban Amurka ya yaba wa gwamnatin Najeriya kan wannan haɗin gwiwa da ci gaban da ake samu."
Ya ce dakarun musamman da suka bar ƙasar sun kammala aikin da aka turo su yi ne kawai, yayin da har yanzu akwai sojojin Amurka da ke horas da jami'an Najeriya.
Trump ya aika wasika ga Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa shugaba Donald Trump na Amurka ya yaba wa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa wajen yaki da ’yan ta’adda bayan kasar sa ta yi magana.
Shugaban na Amurka ya ce dangantakar Amurka da Najeriya na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci, musamman bayan an samu dakarun Amurka da su ka zo Najeriya da kai hare-hare wasu yankuna.
Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Najeriya kan hadin gwiwar tsaro domin dakile ayyukan 'yan ta'adda, yayin da ake hadin gwiwar game da bayanan sirri, sayar da makamai da horas da jam'ai.
Asali: Legit.ng

