Kashim Shettima Ya Duro Najeriya yayin da Ake Ta Jiran Dawowar Tinubu
- Kashim Shettima ya dawo Najeriya bayan wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 da aka gudanar a New York.
- Shettima ya gabatar da jawabin Najeriya, inda ƙasar ta sake neman a yi wa Kwamitin Tsaro na Majilisar Dinkin Duniya garambawul tare da bai wa Afirka kujera ta dindindin
- Mataimakin shugaban ƙasar ya halarci tarurruka kan ilimi, albarkatun ƙasa, ci gaban tattalin arziki da kuma haɗin kan ƙasashen Afirka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da aka gudanar a New York, Amurka.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bar Abuja a ranar 20 ga Satumba domin halartar taron da kuma wakiltar shugaban ƙasar a taron wanda manyan shugabannin duniya ke tattaunawa.

Kara karanta wannan
MURIC ta gano wurare 2 da Najeriya ta yi 'abin kunya' a taron Majalisar ɗinkin duniya

Source: Facebook
Shettima ya gabatar da jawabin Najeriya
Hadimin Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya sanar da dawowar mataimakin shugaban kasar a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2026.
A yayin ziyarar, Shettima ya gabatar da jawabin Najeriya na ƙasa a zaman muhawarar babban taron na UNGA.
A cikin jawabin, Najeriya ta sake yin kira da a yi wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya garambawul.
Najeriya ta buƙaci a bai wa Afirka wakilcin dindindin a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya tare da samar da tsarin ba da tallafin kuɗi na duniya mai adalci.
Ƙasar ta kuma nemi ƙarin tallafin yaƙi da sauyin yanayi da kuma zurfafa haɗin gwiwar ƙasashe ta hanyar tsarin diflomasiyya.
Tinubu ya yi kira kan sarrafa ma’adanan Afirka
Kashim Shettima ya kuma halarci taro na uku na manyan jami’ai na Africa Minerals Strategy Group.
A wajen taron, ya gabatar da matsayar Shugaba Tinubu, wadda ta buƙaci ƙasashen Afirka su daina dogaro da fitar da ma’adanan da ba a tace ba zuwa ƙasashen waje.
Shugaban ya ce ya kamata ƙasashen nahiyar su mayar da hankali kan sarrafa ma’adinai, masana’antu da ƙara darajar albarkatun ƙasa kafin fitar da su zuwa kasuwannin duniya.
Shettima ya gana da ’yan Najeriya
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma gana da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje. A yayin ganawar, ya jaddada muhimmancin gudunmawar ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje wajen ci gaban ƙasa, musamman ta fuskar saka hannun jari, ƙwarewa da hanyoyin sadarwa.
Ya gana da shugabannin ECOWAS da Amina Mohammed Daga cikin sauran muhimman ayyukan Shettima akwai ganawa da sababbin shugabannin Hukumar Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
Ya kuma gana da Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Mohammed.

Source: Facebook
An soki jawabin Najeriya a UNGA
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kungiyar Harkokin Musulmi (MPAC) ta Najeriya ta soki Gwamnatin Tarayya kan rashin ambaton Falasɗinu a jawabin Najeriya a taron UNGA.
Kungiyar ta ce Najeriya ta yi tsokaci sosai kan halin da ake ciki a Gaza yayin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na baya, amma ba ta ambaci Falasɗinu, ko tsarin ƙasashe biyu ba a cikin jawabin da ta gabatar a 2026.
Asali: Legit.ng
