Matukan Tankar Mai Sun Ruga da Gudu a Hormuz yayin da Iran ke Barin Wuta

Matukan Tankar Mai Sun Ruga da Gudu a Hormuz yayin da Iran ke Barin Wuta

  • Ma'aikatan wata tankar mai sun gudu cikin jirgin ceto bayan wani mummunan farmaki da aka kai da makami mai mugun hadari
  • Hukumar UKMTO ta ce lamarin ya faru ne a tazarar mil takwas daga Gabashin Limah na ƙasar Oman, inda ake gudanar da bincike
  • Dakarun juyin juya hali na Iran (IRGC) sun yi ikirarin cewa wasu 'tankoki' biyu sun kama da wuta bayan fashe-fashe da ya faru a teku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Muscat – Ma'aikatan tankar mai da ke ratsa mashigar Hormuz sun gudu daga kan jirginsu zuwa cikin jirgin ceto sakamakon harin wani makami da ba a tantance ba, kamar yadda hukumar kasuwancin teku ta Biritaniya (UKMTO) ta sanar a ranar Talata.

UKMTO ta bayyana cewa ta samu rahotanni da dama a ranar Talata cewa jirgin ya aike da saƙon neman agaji ta tashar VHF Channel 16 bayan samun harin.

Kara karanta wannan

Matasa 9 sun rasu a hanyar neman arziki daga Sokoto zuwa Legas

Mojataba Khamenei da ruwan Hormuz
Mojtaba Khamenei a gefen hagu, jirage a Hormuz a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Reuters ta rahoto cewa UKMTO ta ƙara da cewa jami'in tsaron kamfanin ya tabbatar da cewa ma'aikatan sun fice daga jirgin, kuma babu wani rahoton lalacewa da aka samu a halin yanzu, ko da yake ba a bayyana sunan jirgin ko mamallakinsa ba.

Matsayar dakarun kasar Iran

A gefe guda kuma, rundunar dakarun juyin juya hali na Iran (IRGC) ta bayyana a ranar Talata cewa wasu jiragen ruwa guda biyu na ɗaukar mai sun kama da wuta bayan wasu fashe-fashe a lokacin da suke ƙoƙarin ratsa hanyar Hormuz.

Rundunar ta ce tawagogin ceto suna ƙoƙarin kwashe ma'aikatan daga yankin, ko da yake ba su ambaci sunayen jiragen ba.

Haka zalika, ba a tantance ko jirgin da UKMTO ta ruwaito yana ɗaya daga cikin waɗanda Iran ta ambata ba a bayanin da ta fitar.

Hanyar mashigar Hormuz
Wasu jirage a hanyar mashigar Hormuz da ake takaddama a kanta. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Za a iya tuna cewa Hormuz dake tsakanin Iran da Oman shine babbar hanyar da kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur da gas ɗin duniya ke ratsawa.

Kara karanta wannan

Rikici a APC: Fusatattun masu neman takara a Oyo za su zauna da Tinubu

Rikicin da ya sake ɓullo a farkon watan Yulin 2026 bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ya ƙara haifar da cikas ga harkar sufurin teku.

Gulf Business ta wallafa cewa Iran ta ce za ta ci gaba da rufe hanyar muddin Amurka tana ci gaba da katsalandan game da harkokinta.

Iran ta ce:

"Muddin barnar da Amurka ke yi a wannan shiyya tana ci gaba, za a cigaba da rufe mashigar Hormuz, sannan man fetur, gas, ko takin zamani ba zai fita daga wannan yanki ba."

Trump zai kare Netanyahu

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ba za a taba kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ba a Amurka ta kowace irin hanya ko tsari.

Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICC) ta fitar da sammacin kamu kan Netanyahu a shekarar 2024 sakamakon zargin aikata laifuffukan yaƙi a Gaza.

Trump ya mayar da martani ne kan kalaman Mayor Zohran Mamdani wanda ya ambaci yiwuwar tsare Netanyahu idan ya ziyarci New York domin taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng