Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar da Mutane 3 kan Zargin Hannu a Sace Dalibai a Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar da Mutane 3 kan Zargin Hannu a Sace Dalibai a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu mutum uku kan zargin hannu a sace dalibai da malamai a Oriire da ke jihar Oyo
  • Ana tuhumar su da aikata ta'addanci, boye bayanan 'yan ta'adda, tunzura jama'a da hakar zinari ba bisa ka'ida ba
  • Ana zargin daya daga cikinsu da horas da 'yan ta'adda ta WhatsApp da yada sakonnin tayar da zaune tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta shigar da karar da ta shafi ta'addanci kan wasu mutum uku da ake zargi da hannu wajen sace dalibai da malamai a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Wadanda ake zargin sun hada da Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa (Yunusa bin Musa) da kuma Shamsu Adamu Sani (Abu Itisar).

Kara karanta wannan

Rana ta baci: Ƴan bindiga sun yi arba da ƴan sanda bayan sun sace mutane a Sokoto

Daliban Oyo.
Wasu daga cikin dalibai da malaman Oyo da aka ceto daga hannun yan bindiga Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa an shigar da karar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda 10.

Tuhume-tuhumen sun hada da ta'addanci, garkuwa da mutane, boye bayanan 'yan ta'adda, tunzura jama'a da kuma hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Laifuffukan da ake zargin mutane 3

Takardun karar sun nuna cewa tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2026, wadanda ake zargin sun hada baki da wasu mutum uku da suka hada da Muhammad Sani, Jibril Mohammed da Ibrahim Khabab domin sace dalibai da malamai a Oriire.

Gwamnatin tarayya ta ce hakan ya saba da Sashe na 26(1) na Dokar Hana Ta'addanci ta shekarar 2022.

Ana zargin sun boye bayanan 'yan ta'adda

Masu gabatar da kara sun kuma ce wadanda ake zargin sun boye bayanan mutanen da ake zargin su ne suka shirya satar daliba duk da cewa suna da masaniya kan shirinsu.

A cewar gwamnati, sun kasa sanar da hukumomin tsaro game da shirin da kuma ayyukan wadanda ake zargi, lamarin da ya saba wa Sashe na 16(1) na dokar.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'an tsaron da suka sadaukar da ransu wajen ceto dalibai a Oyo

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta zargi mutanen uku da bayyana kansu a matsayin mambobin kungiyar Darul Salam, wadda ta ce tana da alaka da kungiyar Ansaru da gwamnatin Najeriya ta haramta.

Karin zargi kan Abdulrazak Umar

Baya ga sauran zarge-zargen, Abdulrazak Umar na fuskantar karin tuhume-tuhume da suka hada da horas da 'yan ta'adda ta hanyar WhatsApp mai suna "The Oneness of Allah is the Foundation of Peace."

Ana kuma zarginsa da amfani da dandalin wajen yada wa'azi da sakonnin da ke tunzura mambobi su aikata ayyukan ta'addanci, cewar rahoton The Cable.

Kotun tarayya.
Dakarun yan sanda da ke aikin tabbatar da tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: Federal High Court
Source: Getty Images

Bugu da kari, gwamnati ta zarge shi da hakar zinari ba bisa ka'ida ba tsakanin shekarun 2024 zuwa 2026 a yankin Chaza da ke karamar hukumar Suleja ta jihar Neja.

Atiku ya ayi magana ka ceto daliban Oyo

Kun ji cewa 'dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya yaba wa sojoji da jami'an tsaro kan ceto dalibai da malamai 44 da aka sace a jihar Oyo.

Atiku ya bukaci gwamnati ta ci gaba da matsa lamba kan 'yan bindiga har sai an kubutar da duk wadanda ke hannunsu a sassa daban-daban na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262