ICPC Ta Gano Ma'aikatan Bogi 908, 'Yan Sanda ne kan Gaba
- Hukumar ICPC ta gano ma'aikatan bogi 908 a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sama da 50 tare da kwato kusan Naira miliyan 942
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ce ta zo kan gaba da mutum 570 da ake zargin suna karɓar albashi ba tare da aiki ba
- Shugaban ICPC, Musa Aliyu, ya ce binciken ya bankado yadda wasu jami'ai ke saka sunayen 'yan uwansu a tsarin albashi domin karɓar kuɗin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC) ta bayyana cewa ta gano ma'aikatan bogi 908 a kalla a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 50 yayin wani bincike kan tsarin biyan albashi.
Hukumar ta ce ta kuma kwato kusan Naira miliyan 942 da ake zargin an biya a matsayin albashi ga mutanen da ba su cancanci karɓa ba.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN), ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan binciken da hukumar ke yi kan badakalar albashin ma'aikata a hukumomin gwamnatin tarayya.
'Yan sanda sun zo kan gaba
A cewar shugaban ICPC, rundunar 'yan sandan Najeriya ce ta fi kowace hukuma yawan mutanen da ake zargin ma'aikatan bogi ne.
Ya ce binciken ya gano mutum 570 da ake zargin suna karɓar albashi ba tare da yin aikin gwamnati ba.
The Cable ta rahoto Aliyu ya ce:
"A wannan binciken, mun gano mutum 570 da muke zargin suna cikin ma'aikatan bogi da ke karɓar albashi ba tare da aiki ba."
Rahoton ya nuna cewa Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Kasa ta zo ta biyu da mutum 80 da ake zargin ma'aikatan bogi ne.
Sauran ma'aikatun da abin ya shafa
Binciken ICPC ya nuna cewa ma'aikatar ayyuka ta tarayya tana da mutum 56 da ake zargin ma'aikatan bogi ne.
Haka kuma, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya tana da mutum 24, yayin da ma'aikatar tsaro ke da mutum 19.
Ma'aikatar wutar lantarki da ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da zuba jari sun samu mutum 17 kowacce, yayin da ma'aikatar lafiya ke da mutum 15.

Source: Twitter
Ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya kuwa yana da mutum 12 da ake zargin suna cikin ma'aikatan bogi.
ICPC ta kuma sanya ofishin Akanta Janar na Tarayya da ma'aikatar harkokin cikin gida cikin jerin hukumomin da aka samu matsala, sai dai ba ta bayyana adadin mutanen da abin ya shafa ba.
Yadda ake badakalar albashi
Shugaban ICPC ya bayyana cewa ma'aikatan bogi sun hada da sunayen mutanen da ba su yi aikin gwamnati amma ake saka su cikin tsarin albashi domin karɓar kuɗi ba bisa ka'ida ba.
Ya ce a wasu lokuta jami'an gwamnati kan saka sunayen matansu, 'ya'yansu ko wasu 'yan uwa a cikin tsarin albashi domin su ci gaba da karɓar kuɗin gwamnati.
Aliyu ya ce binciken ya gano wani mutum da ya saka sunan matarsa, ɗansa da surukarsa cikin tsarin albashi, sannan yana karɓar albashin wasu ma'aikata 12.
Ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da bincike domin gano duk masu hannu a wannan badakala tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.
An kama 'yan sanda a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda ta cafke jami'anta huɗu da ake zargin sun karɓi N53,000 ba bisa ka'ida ba daga shugaban ICPC, Musa Aliyu.
Kwamishinan 'yan sandan FCT, Ahmed Sanusi, ya bayyana jami'an a matsayin "ɓarayi" da ba su cancanci sanya kayan aikin 'yan sanda ba,
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa Ahmed Sanusi ya yi magana yana mai cewa an riga an tsare su domin fuskantar hukunci.
Asali: Legit.ng


