Kamfanin da Atiku Ya Dauko Haya Sun Fara Kai Bayanan Tinubu wajen Trump a Amurka

Kamfanin da Atiku Ya Dauko Haya Sun Fara Kai Bayanan Tinubu wajen Trump a Amurka

  • Atiku Abubakar ya dauki hayar kamfanin Von Batten a kan kudi $1.2m domin a fallasa masa Bola Tinubu a kasar Amurka
  • Yanzu wannan kamfani ya gabatar da takardun da suka shafi shari'ar shugaban na Najeriya ga jami’an kasar wajen
  • Von Batten ya mika sama da shafuka 60 na bayanan shari'ar Tinubu, yanzu labarin ya kai ga majalisa da jami'an gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Washington - Kamfanin Von Batten-Montague-York da Atiku Abubakar ya dauko hayarsu sun fara kai wasu bayanai a kan Donald Trump.

Kamfanin Von Batten-Montague-York mai zama a birnin Washington a kasar Amurka ya fara fallasa zargin da ake yi wa Bola Ahmed Tinubu.

Atiku Abubakar
Donald Trump, Bola Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Atiku Abubakar yana aiki da Von Batten-Montague-York

Akwai tuhume-tuhumen da ake yi wa shugaban Najeriya na hannu a badakalar safarar miyagun kwayoyi kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Atiku Abubakar ya dauko hayar wannan fitaccen kamfani a watan Maris a wata yarjejeniyar watanni 12 da za ta ci masa dala miliyan 1.2.

Manufar yarjejeniyar ita ce shawo kan Amurka a tattauna da jami’anta kuma a hure kunnen kasar game da abin da gwamnatin Najeriya ta fada.

Kamfanin ya soma kai wa Amurka bayanan Bola Tinubu

Daga cikin aikin da kamfanin ya fara shi ne ankarar da gwamnatin Donald Trump game da wasu zargi da aka dade ana yi wa Shugaba Bola Tinubu.

Kafin yanzu jami’an gwamnatin Amurka da-dama ba sun zargin da ke wuyan Tinubu ba, don haka kamfanin ya fara bude wa gwamnati wannan zance.

Kamfanin ya bayyana wannan ne a shafin X, ya ce an nuna wa Trump wasu takardun shari’ar shugaba Tinubu da hukuncin da aka yanke a lokacin.

"Bayan tattauna wa da jami’an gwamnatin @realDonaldTrump, ‘yan majalisa da manyan jami’ai, mun fara da gabatar da shafuka fiye da 60 na takardun ma’aikatar shari’a dauke da zargin da ake yi wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu’s (@officialABAT) na hulda da safarar kwayar da aka yi a karshen shekarun 1980s zuwa farkon 1990."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

Zargin harkokin kwaya ya fito fili

Bugu da kari, kamfanin ya fito da wasu takardun ma’aikatar shari’a na safarar kwaya da takardun shari’ar FOIA na shekarar 2023 game da zargin safarar kwayar da ake yi wa Shugaban kasar Najeriya mai-ci, Bola Ahmed Tinubu.

Takardun da kamfanin suka fitar suna zargin wani kamfanin safarar miyagun kwayoyi ya rika jigilar kwayar daga Amurka zuwa Najeria kuma su ka rika kai shi Chicago daga Najeriya, inda ake raba wa ta hannun ‘ya ‘ya da na kusa da kungiyar.

Bayanan da aka fitar sun kunshi har da lambar asusun bankin Mai girma Bola Tinubu. Kuma ana zargin ya bude asusu a bankuna rututu.

Tuhumar ta hada da amfani da wadannan asusu a bankuna wajen hulda da kudin kwayoyi tsakanin shekarar 1988 da 1991 a kasar Amurka.

Rahoton ya ce sauran wadanda sunayensu ya fito su ne Adegboyega Mueez Akande da Abiodun Agbel.

Shari’ar da aka yi da Tinubu har ya rasa wasu kudinsa a Amurka sun fito fili lokacin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi karar zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2026: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da boye Naira tiriliyan 12.8

Atiku ya ji dadin sakamakon zaben Amurka

A 2024 an ji labari sohon mataimakin shugaban kasar Najeriya,Atiku Abubakar, ya taya Donald Trump murnar lashe zaben kasar Amurka.

Atiku wanda ya dade yana neman shugabanci a Najeriya ya bayyana cewa jajircewar Trump abin koyi ne ga 'yan siyasa a fadin kasashen duniya.

Sannan ya bukaci Gwamnatin Donald Trump da ta sa ido domin tabbatar da an yi sahihin zabe mai kyau a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng