Ana Zargin Tinubu Ya Ware Biliyoyi domin Gyara Fadodjin Sarakuna, Atiku Ya Ɗauki Zafi
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kalubalanci gwamnatin Tarayya kan ware biliyoyi saboda masarautu
- Ya ce kundin tsarin mulkin 1999 bai ba gwamnatin Tarayya ikon kula ko daukar nauyin cibiyoyin gargajiya ba, sai gwamnatocin jihohi kawai
- Atiku ya bukaci a bayyana jerin fadojin, wurarensu, kudaden da aka ware, tsarin bayar da kwangila da hujjar kundin tsarin mulki kan aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban kasa a ADC Atiku Abubakar ya sake dura kan gwamnatin Bola Tinubu.
Atiku ya tambaya wane sashe na kundin tsarin mulki ya bai wa gwamnatin Tarayya damar ware Naira biliyan 22.15 daga Asusun Tarayya domin ginawa da gyaran masarautu 106.

Source: Getty Images
Rahoton Vanguard ya ce Atiku ya tambayi wane kundin tsarin mulki Shugaba Tinubu ke aiki da shi.
A cewarsa, kundin tsarin mulkin 1999 bai kafa cibiyoyin gargajiya ba, bai ware musu kudade ba, kuma bai dora wa gwamnatin Tarayya alhakin gudanar da harkokinsu ba.
Ya ce abin da kundin ya tanada kawai shi ne bai wa jihohi damar kafa Majalisar Sarakuna domin ba gwamnoni shawara kan sarauta da dokokin al'ada.
Dan siyasar ya ce bayan wannan iyakacin tanadi, kundin tsarin mulki ya bar kafa, gudanarwa da daukar nauyin cibiyoyin gargajiya a hannun gwamnatocin jihohi da majalisunsu.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu ba zai iya amfani da dokar kasafin kudi wajen karbar ikon da kundin tsarin mulki bai ba gwamnatin Tarayya ba.
Atiku ya ce abin ya kara muni saboda gwamnatin Tarayya ba ta bayyana sunayen sarakunan gargajiya, wuraren ayyukan da kuma al'ummomin da fadojin suke ba.
Ya bayyana hakan a matsayin wata hanya da za ta iya bude kofar cin hanci da rashawa.

Source: Facebook
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu
Atiku ya ce wannan boye-boye ya haifar da zargin cewa watakila ayyukan suna takarda ne kawai, cewar rahoton Punch.
Ya kuma ce akwai yiwuwar sarakunan gargajiyar da aka ware kudaden da sunansu ba za su amfana da su ba.

Kara karanta wannan
Da gaske gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Naira tiriliyan 80? Minista ya yi martani
Atiku ya ce kasafin kudin kasa ba takardar kudi kawai ba ce, illa wata takarda ce ta doka da dabi'a wadda ke nuna abubuwan da gwamnati ta fifita da kuma yadda take tafiyar da mulki.
Ya ce sarakunan gargajiya sun cancanci mutunci da girmamawa, don haka bai dace a yi amfani da su wajen kare rabon kudaden kasafi da ke cike da rashin bayyana gaskiya da kuma tambayoyin da suka shafi kundin tsarin mulki ba.
A karshe, Atiku ya bukaci Fadar Shugaban Kasa, Ofishin Kasafi da dukkan Ma'aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnati su gaggauta fitar da cikakken jerin fadoji 106, wurarensu, adadin kudin da aka ware wa kowane aiki, hujjar kundin tsarin mulki da kuma yadda za a bayar da kwangilolin.
Atiku ya bukaci Tinubu ya yi murabus
An ji cewa Atiku Abubakar ya ce sabanin bayanan OAGF da CBN kan asusun PFIPC ya fallasa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya bukaci a gayyaci Akanta-Janar na Tarayya da Gwamnan CBN su bayyana tare a gaban kwamitin bincike.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce idan Tinubu ya kasa dawo da amincewar jama'a, ya kamata ya nemi afuwa ya kuma yi murabus.
Asali: Legit.ng
