Kasafin Kudin 2026: Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Boye Naira Tiriliyan 12.8

Kasafin Kudin 2026: Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Boye Naira Tiriliyan 12.8

  • Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta boye Naira tiriliyan 12.8 a kasafin 2026, yana zargin hakan barazana ce ga gaskiya da rikon amana
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin Tinubu ta bayyana dalla-dalla yadda za a kashe kudaden Service-Wide Vote da aka ware
  • Atiku ya bukaci Majalisar Tarayya ta binciki dukkan kudaden Service-Wide Vote domin tabbatar da gaskiya da kare dukiyar al’umma daga almubazzaranci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana kasafin kudin tarayya na shekarar 2026 a matsayin mafi muni wajen karya ka’idojin gaskiya da rikon amana a tarihin dimokuradiyyar Najeriya.

Atiku ya yi wannan zargi ne bayan bayyana wasu bayanai da ya ce sun nuna yadda aka boye makudan kudade karkashin Service-Wide Vote (SWV) a kasafin kudin bana.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An yi hasashen gwamnan da zai lallasa Shugaba Tinubu

Atiku Abubakar ya bukaci Tinubu ya yi bayani game da Naira tiriliyan 12.8 da ya ce an boye a kasafin 2026
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (hagu) da Alhaji Atiku Abubakar (dama). Hoto: @officialABAT, @atiku
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce bayanan sun nuna cewa kaso 84 cikin 100 na kasafin 2026 ya ta’allaka ne kan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi 10 kacal, in ji rahoton Daily Trust.

Atiku ya bukaci Tinubu ya yi bayani

Ya ce daga cikin hakan, an ware Naira tiriliyan 12.8 a karkashin Service-Wide Vote na Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, abin da ya ce na nuna yiwuwar kashe kudade ba tare da cikakken bayani ba.

Atiku ya ce Service-Wide Vote ya tashi daga Naira biliyan 638 a kasafin 2025 zuwa Naira tiriliyan 12.8 a kasafin 2026, wanda ya ce karin kusan kashi 1,918 cikin shekara guda ne.

Ya ce shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kamata ya bayyana wa ’yan Najeriya yadda aka yi wannan karin da kuma inda za a kashe kudaden.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Lokacin da Tinubu ya mika wa Shettima fom din zama abokin takararsa a 2027

A cewarsa, babu wata gwamnati mai gaskiya da za ta boye irin wadannan makudan kudade ba tare da bayyana masu cin gajiyarsu da tsarin kashe su ba.

Ya kara da cewa idan gwamnati ta kasa yin bayani, ’yan Najeriya za su iya zargin cewa an ware kudaden ne domin anfani da su wajen shirye-shiryen siyasar APC da kuma zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Tambayoyi kan kudn albashin ma'aikata

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma nuna damuwarsa kan yadda Ma’aikatar Kudi ke da kasafin albashi na Naira biliyan 54.8 kacal, yayin da aka ware Naira tiriliyan 2.19 na albashi karkashin Service-Wide Vote a Ma’aikatar Kasafi.

Ya tambaya su waye ma’aikatan da za su karbi wannan adadi, inda suke aiki da kuma hukumomin da suke karkashinsu.

A cewarsa, wannan ba kasafi ba ne, illa wata babbar tambaya da ke bukatar amsa daga gwamnati, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Atiku ya ce akwai cin amana kan yadda ake zargin an boye tiriliyoyin Naira daga kasafin 2026.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hadu da Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Ya bukaci Majalisa ta bincika

Atiku ya ce abin mamaki ne yadda kudaden da aka boye karkashin Service-Wide Vote suka zarce jimillar kasafin ilimi, tsaro da noma.

Kara karanta wannan

Duk da adawarsu da Tinubu, an yi abin da sai da Atiku da Obi suka yaba masa

Daga karshe, ya bukaci Majalisar Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan dukkan kudaden da aka ware karkashin Service-Wide Vote, musamman Naira tiriliyan 2.19 da aka ware domin albashi.

Ya ce dole ne gwamnati ta bayyana masu cin gajiyar kudaden, dalilin ware su da kuma yadda za a kashe kowace kobo domin dawo da amincewar jama'a kan tsarin kasafin kudin Najeriya.

Atiku ya aika tambaya ga Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Alhaji Atiku Abubakar ya sake caccakar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda ake kashe kudin jama'a.

Dan takarar shugaban kasa na ADC ya bukaci Tinubu ya yi wa yan Najeriya karin haske kan rahoton IMF da ya nuna 2% na tattalin arzikin Najeriya na sulalewa.

Atiku wanda kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne ya ce lamarin ya wuce kuskuren lissafi kawai, dole akwai wani boyayyen al'amari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com