Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Kashe Wani Malami da Bayin Allah da Dama

Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Kashe Wani Malami da Bayin Allah da Dama

  • Yan bindiga sun kashe limamin wata cocinnBaptist da wasu mutane tara a hare-hare daban-daban a Barakin-Ladi da Riyom da ke jihar Filato
  • Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane shida bayan an kai wa fasinjojin da ke tafiya daga kauyen Gana-Ropp hari
  • Wadannan sababbin hare-haren sun sanya tsoro ya karu a tsakanin mazauna yankunan kananan hukumomi biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Wani malamin Cocin Baptist da wasu mutane tara sun rasa rayukansu tsakanin daren Asabar zuwa safiyar Lahadi bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hare-hare a jihar Filato.

An ruwaito cewa maharan sun kashe limamin cocin tare da mutane 9 ne a kauyukan da ke yankin karamar hukumar Barkin Ladi.

Plateau.
Taswirar jihar Filato da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Nigerian Tribune ta gano cewa maharan sun kai hari kan fasinjojin da ke tafiya zuwa Gana-Ropp a Barakin-Ladi a yammacin Asabar, inda suka kashe mutane shida tare da jikkata wasu da ke cikin motar.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga ke hada hadar kudi ta POS, an kama mai taimaka masu

Wani mazaunin yankin da ya shaida lamarin, Ukasha Garba, ya ce mutanen shida da aka kashe fasinjoji ne daga kauyen Gana-Ropp, wadanda ke tafiya zuwa aikin gona.

Yan bindiga sun kashe fasto

An kuma gano cewa a sanyin safiyar jiya Lahadi, yan bindiga suka yi wa wani fasto na Cocin Baptist, sakatarensa da wani mutum guda kwanton bauna tare da harbe su har lahira a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa coci a Dorowa Babuje.

Lamarin ya kawo cikas ga gudanar da ibadar Lahadi a wasu garuruwa da ke makwabtaka, yayin da mutane suka fasa zuwa coci saboda fargabar sake kai wasu hare-hare.

Haka kuma, an ruwaito cewa an kashe wata mata a daren Asabar a Beaten Wereng da ke karamar hukumar Riyom, yayin da aka kashe wani mutum a gundumar Ratyidiin Fan.

Kungiyar BYM ta yi Allah wadai

Sakataren yada labarai na kungiyar Berom (BYM) ta kasa, Rwang Tengwong, ya tabbatar da hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin abin damuwa kuma abin da ba za a amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun turo saƙo kan malaman musulunci 6 da suka sace, sanata ya tsoma baki

Ya ce:

“Mun yinAllah wadai da wadannan hare-hare da kakkausar murya, kuma muna kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta karfafa matakan tsare al'umma. Dole ne a kawo karshen kashe-kashen mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”

Ya yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa kan hare-haren, tare da kama wadanda ke da hannu a ciki da gurfanar da su a gaban kotu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sanda lokacin da suke duba kan titi bayan tashin wani bam a Zamfara Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Tengwong ya kuma bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa cikin shiri, yayin da ya yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakan kariya tun kafin a sake kai hare-hare.

Yunkurin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Alfred Alabo, bai yi nasara ba, domin ba a same shi ta wayarsa ba.

Yan bindiga sun kashe mutane a kasuwa

Kun ji cewa ‘yan bindiga sun kai hari wata kasuwar amfanin gona da ke Mangu, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama.

Mazauna garin Mangu sun ce harin ya faru da misalin karfe 8.30 na dare, lokacin da ‘yan kasuwa da masu sayayya ke shirin rufe kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262