Abin Boye Ya Fito: Yadda aka Budewa Ma'aikatar Bogi Asusun Banki a CBN
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa ya buɗe asusun kuɗin waje guda biyu ga Hukumar PFIPC da ake zargin ta bogi ce
- CBN ya ce an buɗe asusun ne bayan samun umarni daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya, amma ba a taɓa amfani da su ba
- Bayanin CBN ya saɓa da ikirarin Akanta Janar na kwanakin baya, wanda ya ce ba a buɗe wani asusun banki da sunan PFIPC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ya buɗe asusun kuɗin waje guda biyu ga Hukumar PFIPC, wadda ake zargin babu ita a hukumance.
Bankin ya bayyana hakan ne a yayin zaman sauraron ra'ayoyin jama'a da Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai ke gudanarwa domin binciken yadda aka kafa hukumar PFIPC da yadda ta gudanar da ayyukanta.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya nuna cewa zaman ya bankado gibi a tsarin gudanar da aiki da ya bai wa wata hukuma da ake zargin ta bogi damar samun gatan da ake tanada wa hukumomin gwamnati.
Bayanin da CBN ya yi
Daraktan Sashen Ayyukan Banki na CBN, Hamisu Ibrahim, wanda ya wakilci bankin, ya shaida wa kwamitin cewa an buɗe asusun dala da kuma fam na Birtaniya ne bayan samun takardar izini daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya.
A cewarsa, a ranar 30 ga Yulin 2025 ne CBN ya karɓi umarnin da aka rubuta ranar 29 ga Yuli daga ofishin Akanta Janar domin buɗe asusun ga hukumar bogin.
Ya bayyana cewa tsarin CBN na buɗe asusu yana buƙatar samun umarni daga Ofishin Akanta Janar, sannan a tabbatar da sahihancin takardar kafin a aiwatar da buƙatar.
Ba a yi aiki da asusun ba
Sai dai Hamisu Ibrahim ya bayyana cewa bayan buɗe asusun, babu wanda ya zo domin kammala sauran matakan da ake buƙata.
Ya ce ba a dauki bayanan yatsun hannu ba da takardar amincewa ko sunayen jami'an da za su kula da asusun da aka ce na ma'aikatar bogin ba ce.
Saboda haka, ya ce asusun biyu sun kasance babu ko sisi tun daga ranar da aka buɗe su, ba tare da an taɓa saka kuɗi ko cire kuɗi daga cikinsu ba.

Source: Facebook
Bayanin ya saɓa da na Akanta Janar
Bayanin da CBN ya bayar ya saɓa da abin da Akanta Janar, Shamseldeen Ogunjimi, ya faɗa a baya da matsayar gwamnatin tarayya.
Daily Trust ta wallafa cewa Akanta Janar ya yi ikirarin cewa ba a buɗe wani asusu da sunan PFIPC ba, lamarin da ya ƙara haifar da tambayoyi kan yadda aka gudanar da harkokin hukumar.
PFIPC: ICPC ta gayyaci Gbaja
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya gurfana a gaban Hukumar ICPC domin amsa tambayoyi kan zargin kafa hukumar PFIPC.
Lauyan Gbajabiamila, Jiti Ogunye, ya bayyana cewa ya amsa gayyatar hukumar ne bisa umarnin shugaba Bola Tinubu, wanda ya ba ICPC umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ce shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasar ya ba da cikakken haɗin kai ga masu bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Asali: Legit.ng

