Majalisar Kano Ta Matsa kan Binciken Yadda ake Kashe N25m Na Tsaro bayan Hare Hare
- Majalisar dokokin Kano ta shiga damuwa saboda karuwar hare-hare da ake samu a iyakokin jihar da makwabtanta da ke Arewa maso Yamma
- Ta fara daukan mataki, musamman wurin binciken yadda ake samun hare-hare domin a samo hanyar warware matsalar baki dayanta a iyakokin jihar
- Kafin a kai ga warware matalar duka, 'yan majalisar sun kuma bukaci gwamnati ta kara jami'an tsaro da kayan aiki domin dakile matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci a gudanar da bincike kan yadda ake amfani da kudin tsaro na wata-wata da ake ware wa kananan hukumomi.
Wannan bukata ta biyo bayan karuwar hare-haren da ake zargin 'yan bindiga suna kai wa al'ummomin da ke kan iyakar jihar.

Source: Facebook
Leadership ta kawo labarin cewa matsayar ta fito ne a zaman majalisar na ranar Talata, 22 ga watan Yuli, 2026 bayan dan majalisar mai wakiltar mazabar Ghari/Tsanyawa, Garba Ya'u Gwarmai, ya gabatar da kudirin gaggawa.
Rashin tsaro: Yan najalisar Kano sun dauki mataki
Gwarmai ya bayyana cewa al'ummomin karamar hukumar Tsanyawa sun dade suna fuskantar hare-hare, lamarin da ya ce yana kawo cikas ga noma, ilimi, harkokin lafiya da kasuwanci.
Ya ce sabon harin ya faru ne a kauyen Yan Cibi da ke gundumar Yan Kame, inda wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka yi yunkurin sace mutane tare da kwashe dabbobi. Sai dai jami'an tsaro sun dakile harin.
Dan majalisar ya ce harin ya yi sanadin mutuwar shugaban al'umma kuma jami'in kungiyar sintiri, Malam Yusuf Adamu. Ya kuma ce wasu mazauna yankin sun samu raunukan daga harbin bindiga.
Majalisar Kano na neman kananan hukumomi
Gwarmai ya yaba wa sojoji da 'yan sanda bisa yadda suka kwato yawancin shanun da aka sace. Duk da haka, ya ce yanayin dajin da ke kan iyakar Katsina ya hana jami'an tsaro bin maharan da suka tsere.
A cewarsa, hare-haren da ake ci gaba da fuskanta sun tilasta wa mutane da dama barin gidajensu, yayin da wasu kuma suka daina zuwa gonaki saboda tsoron hare-hare.

Source: Facebook
Ya bukaci gwamnatin Kano da gwamnatin tarayya su kara tura jami'an tsaro tare da samar masu da isassun kayan aiki domin kare al'ummomin da abin ya shafa.
Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da kudin tsaro da ake bai wa kananan hukumomi duk wata, yana mai cewa duk da kasancewar wadannan kudade, sojojin da ke aiki a yankin na fama da karancin tallafi.
Gwarmai ya tuna cewa tun farko majalisar ta umarci shugabannin kananan hukumomin su gabatar da rahoton yadda suka kashe kudin tsaron, amma har yanzu ba su bi wannan umarni ba.
Bayan tattaunawa, majalisar ta umurci kwamitin da ya dace ya tabbatar da cewa karamar hukumar da abin ya shafa ta yi cikakken bayani kan yadda aka kashe kudin tsaron, tare da kara sa ido kan yadda ake amfani da su.
Har ila yau, majalisar ta bukaci gwamnatin Kano da gwamnatin tarayya su dauki matakan gaggawa domin dakile matsalar tsaro a garuruwan kan iyaka kafin ta bazu zuwa sauran sassan jihar.
An saki lauyan Kano
A baya, mun kawo labarin cewa rahotanni daga jihar Kano sun tabbatar da cewa yan bindiga sun sako Barista Hashim Abdullahi bayan shafe makonni su na tsare da shi da yanka masa kudin fansa.
Masu garkuwa da mutanen da su ka rike jami'in shari'ar sun sake shi ne bayan iyalansa sun tattaro abin da su ke da shi an biya kudin fansa, sai ba a tabbatar da miliyoyin da su ka biya ba.
Yan bindiga sun yi ram da Baristan ne a lokacin da ya ke hanyarsa ta zuwa jihar Sokoto, inda daga bisani aka tuntubi yan uwansa tare da neman a biya kudin fansa Naira miliyan 20, kafin a rage zuwa N10m.
Asali: Legit.ng


