Kano: Kwanaki 21 da Shiga Hannun Ƴan Bindiga, Lauya Ya Shaki Iskar Ƴanci
- Rahotanni daga jihar Kano sun tabbatar da cewa yan bindiga sun sako Barista Hashim Abdullahi bayan shafe makonni su na tsare da shi
- Masu garkuwa da mutanen da su ka rike jami'in shari'ar sun sake shi ne bayan iyalansa sun tattaro abin da su ke da shi an biya kudin fansa
- Yan bindiga sun yi ram da Baristan ne a lokacin da ya ke hanyarsa ta zuwa jihar Sokoto, inda daga bisani aka tuntubi yan uwansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Barrista Hashim Abdullahi ya samu 'yancinsa bayan ya shafe kwanaki 21 a hannun masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da shi yayin da yake tafiya zuwa jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa an sako lauyan ne bayan iyalansa tare da wasu masu fatan alheri sun biya wani adadin kudin fansa, duk da cewa ba a bayyana adadin da aka biya ba.

Source: Original
Jaridar Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa an yi garkuwa da Barista Hashim Abdullahi ne kwanaki 21 da suka gabata lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Sokoto.
Yadda aka yi garkuwa da lauyan Kano
A ruwayar Daily Post, lauyanya baro jihar Kano ne bayan halartar taron kungiyar lauyoyin Musulmi ta Najeriya (MULAN), inda ya yi hanyar zuwa Sokoto kafin masu garkuwa suka tare shi.
Tsohon shugaban kungiyar MULAN na kasa, Barista Saidu Muhammad Tudun wada, ya tabbatar da sakin lauyan, yana mai cewa yanzu haka ya koma cikin iyalansa lafiya.
Ya ce:
"Gaskiya ne, an sako shi daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi."
Kano: An biya wa lauya kudin fansa
Barista Saidu Muhammad Tudun wada, ya gode wa yan uwa da abokan arziki da suka taya yan uwa da na kusa da lauyan jimami a wadannan akwanaki.
Ya kara da cewa:
"Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa rahamarsa. Haka kuma muna godiya ga dukkan wadanda suka yi mana addu'a, suka nuna damuwa da kuma bayar da goyon baya a wannan lokaci."

Source: Facebook
Kafin a sako Barrista Hashim Abdullahi, rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun fara neman kudin fansa har N100m daga iyalansa.
Sai dai daga baya an ce sun rage bukatar zuwa N10m, tare da bai wa iyalansa wa'adin sa'o'i 48 domin su cika sharadin biyan kudin.
Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka gudanar da sakin lauyan ko kuma inda aka sake shi ba.
'Yan bindiga sun kai hari Kano
A baya, mun kawo labarin cewa ana zargin ‘yan bindiga sun kashe basaraken kauyen Taka-tsaba da ke yankin karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano a wani yanayi da ya jefa jama'a a cikin firgici.
Rahotanni sun ya nuna cewa mutane da dama, galibi mata da yara sun tsere daga Zakawa da wasu kauyuka zuwa garin Tsanyawa doin su fake har harin da aka kai masu ya lafa su kua tsira da ransu.
Haka kuma rahoton ya tabbatar da cewa maharan sun kai hari kauyen Zakawa da ke gundumar Yankamaye tare da wani kauye a karamar hukumar, inda suka yi awon gaba da shanu sama da 100.
Asali: Legit.ng

