Ana Zargin Yaran Dogo Gide Sun Rage Mugun Iri, an Hallaka Hatsabibin Dan Bindiga

Ana Zargin Yaran Dogo Gide Sun Rage Mugun Iri, an Hallaka Hatsabibin Dan Bindiga

  • Rahotanni sun ce an kashe fitaccen shugaban 'yan bindiga a Anka, amma ana samun sabanin bayanai kan yadda mutuwarsa ta faru
  • Wasu sun ce mayaƙan Dogo Gide ne suka kashe shi a kasuwa, yayin da wasu rahotanni ke cewa jami'an tsaro ne suka hallaka shi
  • Bayan mutuwarsa, an ce an kai sababbin hare-hare a Tsafe inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da fiye da mutum 60

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Anka, Zamfara - Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar wani hatsabibin dan bindiga da ya addabi al'ummar jihar Zamfara.

An ce an kashe Kachalla Sani Yellow, daya daga cikin fitattun shugabannin 'yan bindiga a Zamfara, lamarin da ya kawo karshen tasirinsa a yankunan Arewa maso Yamma.

An hallaka shedanin dan bindiga a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da matsalar yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Sai dai ana samun sabanin rahotanni kan yadda aka kashe shi, domin wasu na cewa mayaƙan wani shugaban 'yan bindiga ne suka hallaka shi, cewar Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bangar siyasa suka hallaka wani fitaccen malamin Islamiyya a Bauchi

An yi hasashen yadda aka kashe Yellow

Majiyoyi daga yankin sun ce an kashe Sani Yellow ranar Juma'a, 10 ga Yuli, a kasuwar Dan Jibga da ke karamar hukumar Anka.

Rahotannin sun bayyana cewa wasu dauke da makamai da ake zargin mabiyan Dogo Gide ne sun yi masa kwanton bauna tare da kashe shi da rana tsaka.

Mazauna yankin sun ce wannan na nuna yadda rikicin cikin gida tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga ke kara tsananta a Zamfara.

Dan bindiga ya rasa ransa a Zamfara
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da kwamandan sojoji a Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

An bayyana rawar sojoji a kisan Yellow

Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun ce an kashe Sani Yellow ne yayin wani samame da jami'an tsaro suka gudanar a karamar hukumar Anka.

Majiyoyin sun ce dakarun tsaro sun gudanar da aikin tare da hadin gwiwar 'yan sintirin Maiduguri domin murkushe 'yan bindiga.

Sun kara da cewa samamen na daga cikin hare-haren da ake ci gaba da kai wa maboyar 'yan bindiga domin kawar da manyan shugabanninsu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su tabbatar da wane daga cikin bayanan ne ya fi dacewa da yadda lamarin ya faru ba.

Kara karanta wannan

Matashi mai shekaru 23 ya hallaka Farfesa da kaninsa cikin wani irin yanayi

Duk da haka, mutuwar Sani Yellow na daga cikin manyan ci gaban da aka samu a yakin da ake yi da 'yan bindiga a Arewa maso Yamma.

An dade ana zargin Sani Yellow da jagorantar hare-hare, sace mutane domin neman kudin fansa, satar shanu da kuma tilasta dubban mutane barin gidajensu.

A wani bangaren kuma, an ce wasu dauke da makamai da ake zargin mabiyan Adamu Aliero ne sun kai sababbin hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Tsafe.

Dogo Gide ya gwabza da mayakan Boko Haram

A baya, kun ji cewa tantirin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya tsallake rijiya da baya bayan mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Sadiku sun yi masa kwanton ɓauna.

Dogo Gide ya bayyana cewa ya yi nasara kan ƴan ta'addan inda ya kashe aƙalla guda 20 daga cikinsu tare da ƙwato makamai.

Dangantaka ɗai ta yi tsami ne tsakanin Dogo Gide da ƴan Boko Haram tun bayan da aka kashe masa ɗan uwansa a shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.