Sojojin Sun Rikata 'Yan Boko Haram a Kananan Hukumomin Borno 5

Sojojin Sun Rikata 'Yan Boko Haram a Kananan Hukumomin Borno 5

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin suna kai wa 'yan ISWAP bayanan sirri a wurare daban-daban a Borno
  • Wani ɗan ISWAP ya miƙa wuya a Konduga, inda ya amsa cewa da shi aka kai hare-hare uku a Delwa kafin ya jefar da bindigarsa a cikin kogi
  • Sojojin Najeriya sun kuma gano tare da lalata wasu abubuwan fashewa da aka birne a wani fili kusa da yankin Dagari, cikin Dajin Sambisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Borno – Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun samu nasarar cafke wasu da ake zargin masu kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri.

Bugu da kari, ana zargin wadanda aka kaman suna cikin wadanda ake zargi suna kaiwa 'yan ta'adda kayan da suke amfani da su a daji.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara taso Najeriya a gaba game da kare rayukan kiristoci

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu dakarun Najeriya a cikin daji suna farautar 'yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Wanda aka kama a Mafa

A cewar wani rahoto da masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X, dakarun Bataliya ta 195 tare da jami'an CJTF sun kama wani mutum a unguwar Dusuman da ke karamar hukumar Mafa.

Ana zarginsa da kai wa 'yan ISWAP da JAS bayanan sirri kan zirga-zirgar sojoji ta hanyar kai masu rahoto a ƙauyen Labe.

Konduga: Dan ta'adda ya saduda

Har ila yau, a karamar hukumar Konduga kuma, wani ɗan kungiyar ISWAP ya miƙa kansa ga dakarun Bataliya ta 73.

A yayin bincike, ya amsa cewa da shi aka kai hare-hare uku a Delwa, sannan ya bayyana cewa kafin ya miƙa wuya ya jefa bindigarsa kirar AK-47 a cikin wani kogi.

Vanguarda ta wallafa cewa kayan da aka samu tare da shi sun haɗa da keken hawa, lauje, kayan gyaran keke da kuma tsabar kuɗi kimanin N6,500.

Kara karanta wannan

An kama mai ciki tana kai wa ƴan Boko Haram da ISWAP kayan aiki a Borno

An kama wani a Gubio

A wani samame kuma, dakarun Bataliya ta 149 sun kama wani mutum da ake zargin mai kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri ne a karamar hukumar Gubio.

A cewar sojoji, mutumin ya amsa cewa shi ne ya jagoranci shigowar 'yan ta'adda cikin Gubio a ranar 16 ga Yunin 2026, farmakin da ya yi sanadin kashe wani jami'in CJTF.

Sojoji sun yi nasara a Damboa

Hakazalika, dakarun Bataliya ta 19 sun fatattaki wasu da ake zargin suna kai wa 'yan ta'adda kayan abinci da sauran kayayyaki a kusa da Kauji, cikin karamar hukumar Damboa.

Da suka hango sojojin, sai suka tsere, suka bar kekuna guda biyu, ledojin abin sha, madara, kayan marmari, magungunan dabbobi da kuma lema.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Nasarar da aka samu a Bama

Bugu da ƙari, dakarun sun gano wani abin fashewa da aka birne a wani fili kusa da Dagari, cikin dajin Sambisa da ke karamar hukumar Bama, inda suka lalata shi.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi kukan kura sun kama dan bindiga a jihar Kano

Sojojin sun ce waɗannan nasarori wani ɓangare ne na ƙoƙarin da suke yi na katse hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun bayanan sirri da kayan tallafi, domin ƙara raunana su da kuma inganta tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

An yi hadari kusa da sojoji

A wani labarin, mun kawo muku cewa an tabbatar da mummunan hadarin motar gas a kusa da wajen da sojojin Najeriya suka kafa shinge.

Lamarin ya jawo asarar rayuka akalla shida yayin da motoci suka kone kurmus bayan wuta ta kama da motar gas din ta fashe nan take.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa motocin da suka kone suna da lambobin Legas, Jigawa da birnin tarayya Abuja, kuma ana hasashen daga can suka fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng