Yadda Shari'o'in da Ke gaban Kotuna Ya Kaɗa Hantar Jam'iyyun ADC da NDC

Yadda Shari'o'in da Ke gaban Kotuna Ya Kaɗa Hantar Jam'iyyun ADC da NDC

  • Rikice-rikicen shari'a kan shugabanci, tsarin jam'iyya da rajista sun tayar da hankali a ADC da NDC masu adawa a Najeriya
  • Wasu 'yan takarar ADC sun ce hukuncin kotu ya rage kwarin gwiwar magoya baya, yayin da shugabannin jam'iyyar ke jaddada cewa za su shawo kan matsalolin
  • NDC ma ta tabbatar da cewa karar kotu kan rajistarta ba za ta hana ta shiga zaben 2027 ba, tana mai cewa shari'o'in za su karfafa dimokuradiyyarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rikice-rikicen shari'a kan shugabanci, tsarin jam'iyya da rajista sun haddasa rashin kwanciyar hankali a jam'iyyun adawa.

Jam'iyyun da suka fi shiga tashin hankali su ne ADC da kuma NDC waɗanda ke ƙoƙarin kwace mulki a hannun Bola Tinubu.

Hankalin ADC da NDC ya tashi kan shari'o'in da ke gaban kotuna
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar, Shugaba Bola Tinubu da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu, Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Matsalolin da shari'o'i a kotu ke jawowa

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da damuwa kan yiwuwar tasirin sa ga shirye-shiryensu na babban zaben 2027, cewar Punch.

Kara karanta wannan

NDC, ADC, APC da sauran rigimar cikin gida da ke damun jam'iyyun siyasa a Kano

Bincike ya nuna cewa wasu 'yan takara da mambobin ADC na fargabar cewa yawaitar shari'o'in da ake yi wa jam'iyyar na iya rage saurin ci gabanta.

Sun ce hakan na iya raunana kwarin gwiwar magoya baya da kuma hana sabbin mutane shiga jam'iyyar.

Wasu mambobin ADC da suka nemi a sakaya sunayensu sun bayyana cewa hukuncin kotu da aka yanke kan shugabancin jam'iyyar ya kara haddasa rudani, sun ce bayan hukuncin ne suka fara nuna damuwa kan makomar jam'iyyar.

Yan ADC sun fara korafi kan shari'o'i a kotuna
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Dan majalisar wakilai ya yi korafi

Wani dan takarar Majalisar Wakilai daga Ekiti ya ce shari'o'in suna hana masu ruwa da tsaki karfafa jam'iyyar.

Ya kara da cewa wasu masu kada kuri'a na ganin ADC ba za ta samu damar shiga zaben 2027 ba saboda matsalolin kotu.

Hakazalika, wani dan takarar Majalisar Dokoki daga Osun ya ce masu kada kuri'a na nuna shakku kan makomar jam'iyyar.

A cewarsa, wasu na tsoron kada kuri'unsu su tafi a banza idan kotu ta dauki wani hukunci kan rajistar ADC, cewar Daily Post.

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu, ya zargi APC da kokarin hana ADC ci gaba ta hanyar siyasa da shari'a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutane 3 kan zargin hannu a sace dalibai a Najeriya

Sai dai ya ce jam'iyyar tana da gogaggun shugabanni kuma za ta kare hakkinta ta hanyar doka.

Jam'iyyar ADC na fuskantar kararraki da suka shafi shugabanci da tsarin gudanarwa. Daya daga cikinsu shi ne karar da Nafiu Bala ya shigar yana kalubalantar halaccin kwamitin gudanarwa karkashin David Mark, tare da wasu kararraki kan tarukan jihohi.

A bangaren NDC kuwa, jam'iyyar ta ce kararrakin da suka shafi shugabanci da rajista ba za su hana ta shiga zaben 2027 ba.

Ta bayyana cewa ta daukaka kara kan hukuncin da ya soke rajistarta kuma tana da yakinin cewa adalci zai yi nasara.

An ba ADC shawara kan cin zaɓe

Mun ba ku labarin cewa wata ƙungiyar siyasa ta bukaci jam'iyyar ADC ta zaɓi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa da ke da karɓuwa.

Ƙungiyar ta ce zaɓin kwararren mataimakin shugaban ƙasa, mai farin jini da goyon bayan jama'a zai taimaka wa ADC.

Ta kuma buƙaci shugabannin ADC su fifita haɗin kai, maslahar ƙasa da gina ƙawance tsakanin yankuna domin ƙara samun goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.