2027: Jam'iyyu 3 Sun Makara har INEC Ta Rufe karban Sunayen 'Yan Takara
- Hukumar zabe ta kasa, INEC ta rufe dandalin karɓar sunayen 'yan takara bayan wa'adin ƙarshe ya cika a daren Talata, 14 ga Yuli, 2026
- Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyu uku sun gaza samun damar shigar da ƴan takarar shugaban kasarsu zabe har wa'adin ya cika
- Amma jam'iyyun APC, da haɗakar ƴan adawa na ADC da NDC na cikin jam'iyyun da suka tabbatar da mika sunayen 'yan takararsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta rufe dandalinta na karɓar sunayen 'yan takara bayan cikar wa'adin ƙarshe da aka ba wa jam'iyyu dama.
Sai dai duk da haka, an samu wadansu jam'iyyu uku ba su kammala mika sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu ba a shafin INEC ba.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Mataimakin shugaban APC da wasu manyan ƙusoshi sun fice daga jam'iyyar

Source: Twitter
Wata sahihiyar majiya a INEC, da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana a hukumance, ta shaida wa Daily Trust cewa jam'iyyun da abin ya shafa sun haɗa da tsagin PDP.
Jam'iyyu sun gaza cika umarnin INEC
Business News Nigeria ta kawo labarin cewa bayan tsagin PDP mai biyayya ga Wike, APGA, da kuma tsagin LP ƙarƙashin Nenadi Usman sun gaza sanya sunayen tan takararsu.
Majiyar ta ce kusan dukkan sauran jam'iyyun siyasa masu rijista sun samu nasarar dora sunayen 'yan takararsu kafin hukumar ta rufe shafinta.
An ce hukumar zaben ta INEC ta tsawaita wa'adin ne bayan buƙatun wasu jam'iyyu, tare da jaddada cewa ba za ta sake ƙara wani lokaci ba.
Manyan jam'iyyu sun cika umarnin INEC
Rahotanni sun nuna cewa manyan jam'iyyun adawa da na gwamnati sun kammala mika sunayen 'yan takararsu kafin wa'adin ya ƙare.
Haka kuma jam'iyyar APC ta mai sunayen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima domin neman wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha kaye," An yi hasashen gwamnan da zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Source: Twitter
Haka kuma ADC ta mika sunayen Atiku Abubakar da abokin takararsa Rotimi Amaechi, yayin da NDC ta gabatar da Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.
Sai dai wasu majiyoyi a INEC sun bayyana cewa akwai wasu jam'iyyu da suka gabatar da sunan ɗan takarar shugaban ƙasa kawai ba tare da sunan mataimakinsa ba.
A wasu jihohi kamar Benue, Kwara da Nasarawa kuma, har yanzu ana fuskantar ruɗani kan waɗanne sunaye ne aka amince da su a takarar kujerun Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
INEC ta musanta ikirarin Nafi'u Bala
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta musanta ikirarin cewa shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala ya samu damar shigar da bayanan 'yan takara bayan an ba wa su David Mark.
Shafin INEC ya nuna Sanata David Mark ne halastaccen shugaban ADC na ƙasa, yayin da Rauf Aregbesola ke a matsayin sakatare yayin da rikici ya mamaye jam'iyyar har batu ya kai gaban kotu.
Rikicin shugabanci a jam'iyyar adawa ta ADC na ci gaba da ƙara kamari gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe yayin da Nafi'u Bala ya ja daga wajen adawa da yan adawa da suka shiga jam'iyyun.
Asali: Legit.ng