An Sako Tinubu a gaba Ya Yi Murabus kafin Zaben 2027 Bayan Rahoton Bankin Duniya

An Sako Tinubu a gaba Ya Yi Murabus kafin Zaben 2027 Bayan Rahoton Bankin Duniya

  • ADC ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya manufofinsa na tattalin arziki ko ya sauka daga mulki saboda ƙarin talauci da yunwa a Najeriya
  • Jam'iyyar ta ce rahotannin Bankin Duniya da WFP sun nuna manufofin gwamnatin APC sun gaza wajen inganta rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya
  • ADC ta yi alƙawarin farfaɗo da noma, gyara madatsun ruwa da tabbatar da tsaro idan ta lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja - Jam'iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi watsi da manufofinsa na tattalin arziki da ta ce sun jefa miliyoyin 'yan Najeriya cikin talauci, ko kuma ya sauka daga mulki.

Jam'iyyar ta bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki ba, tana mai zargin gwamnatin APC da fifita alkaluman tattalin arziki kan rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

"Zan yi murabus daga Ministan Abuja"; Nyesom Wike ya kafa sharadin barin ofis

ADC ta bukaci Tinubu ya yi murabus
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: @officialABAT, @BolajiADC
Source: Facebook

Martani kan rahotannin Bankin Duniya da WFP

A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a shafinsa na X a ranar Asabar, ADC ta ce ta damu matuƙa da rahoton Bankin Duniya da ya nuna cewa 'yan Najeriya miliyan 139 na rayuwa a ƙarƙashin layin talauci.

Jam'iyyar ta kuma yi nuni da rahoton Hukumar Abinci ta Duniya (WFP), wanda ya ce mutum miliyan 17 a Najeriya na fama da matsananciyar yunwa, lamarin da ya zama mafi muni cikin kusan shekara goma.

Ta ce waɗannan rahotanni hujjoji ne da ke nuna gazawar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.

Jam'iyyar ta ce manufofin gwamnati sun gaza

ADC ta bayyana cewa ta dade tana gargadin cewa ƙaruwa a kuɗaɗen shiga da ajiyar kuɗaɗen waje ba su da amfani idan ba su inganta rayuwar jama'a ba.

A cewarta, gwamnati ta ci gaba da bin manufofin da ta bayyana a matsayin masu jefa jama'a cikin wahala, tana kiran su "jarumtaka" da "wahalar da ta zama dole."

Kara karanta wannan

An taso Tinubu a gaba game da lafiyarsa kan sake neman takara a 2027

Jam'iyyar ta ce bayan shekara uku a mulki, sakamakon ya bayyana karara, inda ta ce miliyoyin 'yan Najeriya ke cikin talauci da yunwa.

ADC ta bukaci Tinubu ya yi murabus

Jam'iyyar ta ce sakamakon da gwamnatin Tinubu ta samu ya kamata ya sa shugaban ƙasar ya yi tunanin sauka daga mulki maimakon neman wa'adi na biyu a 2027.

A cewarta, Najeriya na buƙatar shugabanci da ke fahimtar halin da jama'a ke ciki tare da fifita jin daɗinsu fiye da ƙawata alkaluman tattalin arziki.

ADC ta bukaci Tinubu ya yi murabus
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a taron TICAD 9 a Japan. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Ta kuma soki abin da ta kira almubazzarancin gwamnati yayin da ake bai wa jama'a tallafin rage raɗaɗin rayuwa.

Abin da ADC ta yi alƙawarin yi idan ta ci zaɓe

ADC ta ce idan ta samu damar kafa gwamnati, za ta aiwatar da gyare-gyaren da za su magance tushen yunwa da talauci.

Karanta sanarwar kakakin ADC a nan kasa:

Melaye ya nemi Tinubu ya yi murabus

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Dino Melaye ya soki jawabin ranar dimokuraɗiyya da hugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a ranar Juma’a, 12 ga Yunin 2026

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Sanata Dino Melaye ya yi magana yana mai bayyana jawabin shugaban kasar a matsayin wanda bai yi daidai da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba.

Tsohon ɗan majalisar dattawan ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar da ya yi murabus saboda tabarbarewar tsaro da ƙaruwar sace-sacen mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com