Matsayar Addinin Musulunci kan Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

Matsayar Addinin Musulunci kan Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

  • Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya tabbatar da cewa IPO na Matatar Dangote ya dace da ka’idojin Shari’a, bayan an gudanar da bincike kan harkokin kamfanin da kudin shigarsa
  • Dogarawa ya ce an tantance IPO din ne bisa ka’idar AAOIFI mai lamba 21, wadda ta tanadi sharudan da kamfanoni ke bukatar cikawa kafin hannayensu su zama halal ga masu zuba jari
  • Binciken ya nuna cewa bashin da ake bin kamfanin mai riba ya kai kashi 13, ajiyar kudin da ke samar da riba bai kai kashi 12 ba, yayin da kudin ruwa bai kai kashi 2% ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya bayyana cewa hannun jarin matatar Dangote ya dace da ka’idojin Shari’a, bayan an gudanar da tantancewa kan kamfanin.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Dogarawa ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin da mutane suka rika yi masa kan ko IPO din da aka fara sayarwa a ranar Litinin 14 ga Satumba 2026 ya dace da Shari’a.

Matatar Aliko Dangote
Sashen Matatar Dangote da ke jihar Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Legit ta gano cewa malamai ya wallafa amsoshin da ya ba jama'a ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Matsayar Musulunci kan IOP

Dogarawa ya ce ya kasance cikin tsarin tantance IPO din ta hannun mai ba kamfanin shawara kan Shari’a, sannan ya halarci wata ganawa tsakanin CBN FRACE, mai ba da shawara kan Shari’a da sauran masu ruwa da tsaki da Hukumar SEC ta shirya.

Ya ce Mataimakin Shugaban FRACE, Sheikh Farfesa Bashir Aliyu Umar, ne ya jagoranci ganawar a madadin Shugaban FRACE, Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh.

Sauran malaman da suka shiga ganawar sun hada da Farfesa Abdurrazaq Alaro na Jami’ar Ilorin, Farfesa Usman Zunnurain na BUK, Farfesa Akram Laldin na Malaysia, Dr Burhan na Bahrain da Dr Omar Oseni na Turkiyya.

Harkokin matatar sun dace da shari’a

Sheikh Dogarawa ya ce an gudanar da tantancewar ne bisa ka’idar AAOIFI Shari’ah, wadda ta kunshi sharudan zuba jari a hannayen kamfanoni.

Kara karanta wannan

Gwamnan Najeriya da ke biyan ma'aikatan shi N500,000 a wata

Ya ce an fara duba harkokin kasuwancin DPRP domin tabbatar da cewa babban aikin kamfanin da sauran ayyukansa sun dace da Shari’a.

Sakamakon binciken ya nuna cewa babban aikin kamfanin da ayyukan da suke tare da shi duk sun halatta, kuma kamfanin ba ya harkar kayayyakin da ba su dace da Shari’a ba.

Dangote a matatar shi
Alhaji Aliko Dangote a matatar shi da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Maganar kudin ruwa a matatar

Sheikh Dogarawa ya ce an kuma gudanar da tantancewar kudi ta hanyar duba bayanan kadarori da basussuka da kuma bayanan kudaden shigar kamfanin da aka tantance.

A karkashin ka’idar, bashin da ake karba da riba bai kamata ya wuce kashi 30% na darajar kasuwar kamfanin ba.

Haka kuma, ajiyar kudi ko jarin da ke samar da riba bai kamata ya wuce kashi 30% na darajar kasuwar kamfanin ba, yayin da kudin shigar da aka samu daga riba bai kamata ya wuce kashi 5% na jimillar kudaden shiga ba.

Bayanin Sheikh Alaro

Malamin addinin Musulunci, Farfesa Abdurrazaq Alaro ya bayyana cewa hannun jarin ya dace da shari'a kuma bai karya doka ba.

A wani bidiyo da Shehu Abdul Salam ya wallafa a Facebook, Sheikh Alaro ya ce sun bi matakan da suka dace domin tantancewa, ya ce suna tantance kamfanoni lura da abubuwa guda uku:

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tinubu ya dauko sabon gyara a dokar haraji ana shirin 2027

1. Duba ko kamfani ba ya alaka da kudin ruwa

2. Duba ko kamfani yana wasu kasuwanci da suka sabawa shari'a

3. Duba ko kamfani yana hada ayyukan halal da haram, musamman ta bangaren kudin ruwa

Bayanin Sarki Sanusi II

A wani labarin, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II, ya gargadi masu shirin zuba jari a IPO na Matatar Dangote da kada su yi amfani da kudaden da suke da muhimmanci kamar kudin makarantar ‘ya’yansu wajen sayen hannun jari.

Sanusi ya shawarci jama’a da su zuba kudin da za su iya warewa na dogon lokaci ba tare da bukatarsu ta gaggawa ba.

Ya ce bai kamata mutum ya sayar da gidan da yake zaune ko ya dauki kudin makarantar ‘ya’yansa ya saka a hannun jari ba, sai dai ya zuba kudin da zai iya warewa kamar N10,000, N20,000 ko N30,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng