Rikici Ya Barke a Fadar Shugaban Kasa kan Nada Dan Arewa Mukami, an Ƙi ba Shi Dama
- Fiye da makonni uku bayan Tinubu ya naɗa Dr Abdulrazak Namdas shugaban BCDA, rikici ya barke a fadar shugaban kasa
- Majiyoyi sun ce har yanzu Namdas bai karɓi takardar naɗi ba, lamarin da ya haddasa rikicin shugabanci a hukumar
- Ana zargin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da riƙe takardar naɗin Namdas, yayin da Dakorinama George ke ci gaba da gudanar da ayyuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanar da naɗin Dr Abdulrazak Namdas a matsayin Darakta Janar na Hukumar Raya Al’ummomin Kan Iyaka (BCDA).
An sanar da nadin ne tun ranar 26 ga Yunin 2026, sai dai har yanzu bai karɓi takardar naɗin hukuma ba.

Source: Facebook
BCDA: Rikici ya barke bayan nadin Namdas
Jinkirin ya haifar da rikicin shugabanci a hukumar, domin tsohon shugaban hukumar, Dakorinama George, yana ci gaba da gudanar da ayyukan ofis duk da sanarwar maye gurbinsa, cewar Punch.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa Namdas ya maye gurbin George, wanda ya yi murabus domin neman wata kujera ta zaɓe.
Sai dai fiye da makonni uku bayan sanarwar, Namdas bai karɓi takardar naɗinsa ba, abin da ya hana shi karɓar ragamar shugabancin hukumar a hukumance.
A halin yanzu, Dakorinama George ya ci gaba da wakiltar BCDA a tarurruka da gudanar da harkokin hukumar kamar yadda aka gani a wata ganawa da Ministan Kuɗi.

Source: Facebook
Zargin da ake yi wa George Akume
Rahotanni sun nuna George ya gana da Ministan Kuɗi domin neman a saki kuɗaɗen ayyukan BCDA tare da gabatar da wasu manyan shirye-shiryen ci gaban yankunan kan iyaka.
Jami’in APC Hamman Yero ya zargi Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da kasa fitar da takardar naɗin Namdas duk da amincewar shugaban ƙasa.
Yero ya ce idan shugaban ƙasa ya amince da naɗi amma ba a aiwatar da shi ba, hakan na tayar da tambayoyi masu muhimmanci kan tsarin mulki da gudanar da gwamnati.
Majiyoyi daga cikin BCDA sun yi zargin cewa George bai miƙa mulki gaba ɗaya ba bayan ya yi murabus domin neman tikitin gwamna a Rivers, cewar Daily Post.
Majiyar ta ce bayan George ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na APC, ya koma hukumar ya ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da wata miƙa mulki ba.
Har ila yau, an yi zargin cewa George na samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda ya taɓa yi masa aiki a Rivers.
Sai dai rahotanni sun ce ba ta samu damar tabbatar da wannan zargi ba, yayin da ɗaya daga cikin abokan George ya bayyana shi a matsayin hasashe kawai.
Da aka tuntubi Bayo Onanuga, ya ce shugaban ƙasa bai canja ra’ayinsa ba, kuma Namdas ne halastaccen shugaban BCDA.
Onanuga ya bayyana cewa alhakin fitar da takardar naɗi yana hannun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, saboda an riga an aika da bayanin naɗin can.
Masanin harkokin jama’a Sunday Awosika ya bayyana cewa lamarin na nuna babbar matsala a tsarin tafiyar da gwamnati idan har zarge-zargen sun tabbata.
Shi kuma Abdulrasaq Rasheed ya ce abin da ke faruwa na nuna rashin daidaitotsakanin ofisoshin Shugaban Ma’aikata da Sakataren Gwamnatin Tarayya.
BCDA: Atiku ya ba Tinubu shawara kan zabe

Kara karanta wannan
Masoyan tsohon minista sun dawo da karfinsu, sun kalubalanci hana shi takarar gwamna
An ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya sake ba Shugaba Bola Tinubu shawara game da zaben 2027.
Atiku ya ce rikicin shugabancin Hukumar BCDA da makamancinsa a NIPOST sun nuna gazawar gwamnati wajen aiwatar da doka.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kamata Tinubu ya mayar da hankali kan magance matsalolin Najeriya.
Asali: Legit.ng

