Peter Obi Ya Sake Bukatar Tinubu Ya Yi Murabus kan Badakalar da IMF Ta Tono

Peter Obi Ya Sake Bukatar Tinubu Ya Yi Murabus kan Badakalar da IMF Ta Tono

  • Asusun bada lamuni na duniya ya fitar da wasu bayanai cewa gwamnatin Bola Tinubu ta kashe wasu kudade da ba su a cikin kasafin kudi
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya nuna damuwa kan yadda aka kashe kudaden ba tare da sahalewar majalisa ba
  • Peter Obi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi murabus daga mukaminsa saboda abin da ya kira cin hanci da rashawa da ya yi wa gwamnatinsa katutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya sake jaddada bukatarsa ta cewa lallai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus.

A wannan karon, Peter Obi ya kafa hujja da cewa sabon bayanin da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar game da kashe kudaden da ba su cikin kasafin kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya burma matsala da aka bukaci ya biya N50bn

Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus
Peter Obi da shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @PeterObi, @aonanuga1956
Source: Twitter

Meyasa Obi ya ce Tinubu ya yi murabus?

Peter Obi ya sake yin kiran ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026.

Ya ce bayanin na IMF ya kara tabbatar da damuwar da ake da ita kan rashin rikon amana, cin hanci da rashawa, da kuma yadda ake gudanar da kudaden kasar a karkashin gwamnati mai ci.

Obi ya gina sabon kiran nasa ne bisa bayanan da IMF ta fitar kwanan nan na cewa kudaden da aka kashe wa jama'a wadanda suka kai kusan kashi 2 cikin 100 na jimillar GDP a shekarar 2025, ba a sanya su a cikin kasafin kudin kasar ba.

A cewarsa, kudaden da aka ruwaito an kashe din, wadanda ya kiyasta sun kai kusan Naira tiriliyan 8.83, an kashe su ne a wajen tsarin kasafin kudin da aka amince da shi, saboda haka ba su samu sanya idon majalisa ko binciken hukumomi ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Obi ya nuna damuwarsa kan bayanin IMF

Yayin da yake bayyana wannan lamari a matsayin "abin tsoro," Obi ya bayyana cewa adadin kudin ya kai fiye da kashi 1 cikin 3 na kasafin kudin manyan ayyuka na kasar na shekarar 2025 wanda ke da Naira tiriliyan 23.96.

Ya ci gaba da cewa adadin kudin ya kuma zarce kudaden da aka ware wa sassan ilimi da lafiya a cikin shekarar kudi ta bana.

“Hukumar IMF ta bayyana yanzu cewa kusan Naira tiriliyan 8.83 da aka kashe a shekarar 2025 ba su bayyana a cikin kasafin kudi ba. Wannan kashe kudi ba a tsara shi ba, saboda haka ba ya karkashin sanya idon majalisa ko binciken hukumomi. Wannan abin tsoro ne."

- Peter Obi

Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya ce ya kamata Tinubu ya yi murabus

Obi ya ce abubuwan da suka biyo baya, musamman bayanan da IMF ta fitar, sun karfafa gwiwarsa na cewa gwamnatin ta gaza a cikin ayyukan da ke kanta.

Kara karanta wannan

Rahoton IMF: Atiku ya aika tambaya ga Tinubu kan 'wanda ke sace 2%' na kuɗaɗen Najeriya

“Bayan bayyana gaskiya ta yau da kullum na yaduwar cin hanci da rashawa a wannan gwamnati da kuma rashin nuna damuwarta gaba daya ga jin dadin jama'a da tsaron 'yan kasa na Najeriya, mataki guda daya tilo mai ma'ana shi ne Shugaba Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa."

- Peter Obi

An bukaci Peter Obi ya biya N50bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa kalaman da Peter Obi ya yi a kan mataimakin shugaban jam'iyyar LP na kasa, Abayomi Ararambi, na neman jefa shi a cikin matsala.

Ararambi ya bukaci Obi ya janye maganarsa a fili, ya ba shi hakuri, sannan ya biya shi Naira biliyan 50 a matsayin diyyar zargin kalaman batanci da ya yi masa a yayin wata hira.

Tawagar lauyoyin Arabambi sun kafa hujjar cewa kalaman na shaci-fadi ne, na keta da kuma batanci ga wanda suke karewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com