Ahmad Gumi Ya Waiwayi Sheikh Jingir saboda Maganar Tallar Tikitin Muslim Muslim

Ahmad Gumi Ya Waiwayi Sheikh Jingir saboda Maganar Tallar Tikitin Muslim Muslim

  • Ahmad Abubakar Mahmud Gumi bai goyon bayan a rika amfani da addini wajen harkokin siyasa a Najeriya
  • Malamin ya yi tsokaci game da kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir wanda yake goyon bayan APC
  • Dr. Gumi ya nema wa Jingir uzuri kuma ya zargi ‘yan adawa da cusa addini a siyasa domin samun kuri’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya tofa albarkacin bakinsa bayan wasu kalamai da aka ji Sani Yahaya Jingir ya yi.

An gayyaci Sheikh Sani Yahaya Jingir ya sa albarka wajen taron auren gata da gwamnatin jihar Kano ta yi a karshen makon jiya.

Dr. Ahmad Gumi
Shugaba a Izala, Sani Jingir da Ahmad Gumi a masallaci a Kaduna Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Jawabin Sani Yahaya Jingir ya fusata jama'a

Kalaman da suka fito daga bakin jagoran na kungiyar Izala sun jawo Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi martani a Facebook.

A wajen taron auren, shugaban na Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ya kawo zancen siyasa, yana tallata APC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya zargi Jingir da rura wutar rikici bayan kalamansa kan Muslim Muslim

Daily Trust ta ce kungioyi da-dama da manyan ‘yan siyasa sun fito sun yi tir da Jingir ganin yadda ya maida zabe tamkar yakin addini.

Martanin da Ahmad Gumi ya yi

Sheikh Ahmad Gumi yana cikin wadanda maganar malamin ba ta yi masu dadi ba, ya kuma bada shawarar a daina cusa addini cikin siyasa.

Babban malamin na fikihun Malikiyyah ya yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir uzuri, yana ganin akwai abin da ya sa yi wannan magana.

Gumi ya bayyana cewa Jingir wanda yake zama a garin Jos da ke jihar Filato yana fama da wadanda suke yi wa Musulunci bakar tsana.

“A yi wa Sheikh Jingir uzuri na wannan tsattsauran ra’ayin nasa a siyasa; tsundum yake cikin kiyayyar da ake yi wa Musulunci. Kwanan nan nadin shugaban jami’a kawai ya jawo rikici”

- Dr. Ahmad Gumi

Garin Jos ya yi kaurin suna tun tuni wajen rikicin addini tsakanin Musulmai da Kiristoci.

Gumi ya cigaba:

"A gefe guda kuma, su ma ‘yan adawa suna amfani da addini wajen samun kuri’u.
"A kasa mai tarin addinai, bai kamata a rika tsumbula adddini cikin kazantar siyasa ba,"

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari zai bude babin 2023 ya tona abin da ya faru lokacin neman takarar APC

Yadda Gumi ya tabo Peter Obi

Ba tare da kiran suna ba, Gumi ya yi amfani da wanni gajeren bidiyo na Peter Obi inda aka ji yana amfani da addini wajen samun nasara a 2023.

An ji Obi wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP a zaben da ya wuce yana kirista ga masu zuwa coci da su tashi su karbe Najeriya.

Tsohon gwamnan Anambran shi kadai ne Kirista a babbar jam’iyya da ya nemi mulki a 2023 lokacin da jam'iyyar APC ta tsaida Musulmi da Musulmi.

Jingir da tikitin Musulmi da Musulmi

Ku na da labarin raddin da minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir a shafinsa.

Jagora a kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya sha raddi daga wajen Solomon Dalung saboda zancen tikitin Musulmi da Musulmi.

'Dan siyasar ya ce tikitin bai taimakai talakan Musulmi ta kowace hanya ba kuma bai kamata a goyi bayan takara kawai ta fuskar addini ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng