An Taso Ministan Tinubu a Gaba Ya Yi Murabus bayan Mutuwar Budurwa a Gidansa
- Jam'iyyar ADC ta nuna damuwa bayan mutuwar wata budurwa a gidan ministan ayyuka a Najeriya
- ADC ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutuwar Mary Habila a gidan ministan
- Ta bukaci Umahi ya ajiye mukaminsa na wucin gadi har sai an kammala bincike, tana mai cewa hakan zai tabbatar da adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta nuna takaici game da mutuwar wata budurwa a gidan minista.
ADC ta kara matsa wa gwamnatin tarayya lamba kan mutuwar Mary Habila A gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, da ke Ebonyi.

Source: Twitter
Hakan na cikin sanarwar da sakataren yada labaran jam'iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, cewar Punch.
ADC ta bukaci Umahi ya yi murabus

Kara karanta wannan
PFIPC: Yadda 'yan sanda suka bankado ma'aikatar bogi a karkashin gwamnatin Tinubu
Jam'iyyar ta bukaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano hakikanin abin da ya faru da marigayiyar a gidan ministan ba tare da tasirin gwamnati ba.
Haka kuma ADC ta bukaci David Umahi ya ajiye mukaminsa na wucin gadi domin bai wa binciken cikakken 'yanci da kuma karfafa amincewar jama'a.
An ce mutuwar wata 'yar Najeriya a gidan minista ya tayar da hankula tare da jawo suka kan gwamnati, cewar Vanguard.
Jam'iyyar ta ce har yanzu akwai tambayoyi kan dalilin kasancewar Mary Habila a gidan ministan da kuma yadda mutuwarta ta faru ba tare da amsoshi ba.
ADC ta bukaci a gudanar da gwajin gawar marigayiyar domin gano musabbabin mutuwarta, sannan a bayyana sakamakon binciken ga jama'a cikin gaskiya.
Jam'iyyar ta zargi gwamnatin Bola Tinubu da kare manyan jami'an gwamnati idan suka shiga cece-kuce, tana cewa hakan yana rage amincewar jama'a da hukumomi.

Source: Twitter
Martanin Umahi kan zargin da ake yi masa
David Umahi ya musanta aikata wani laifi, ya ce Mary Habila tana cikin ma'aikatan lafiya na ma'aikatar ayyuka, kuma ya bukaci iyalanta su amince da gwaji kan gawar.

Kara karanta wannan
PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu
Ya ce iyalan marigayiyar ne suka fara shiga ɗakinta bayan sun damu da rashin jin duriyarta, kafin daga bisani su kai ta asibiti domin ceto rayuwarta.
Ministan ayyukan na Najeriya ya bayyana cewa an sanar da 'yan sanda cikin gaggawa bayan faruwar lamarin.
Ya ƙara da cewa ya ba da umarnin gudanar da binciken gawar domin gano ainihin musabbabin mutuwar, kuma za a yi hakan ne tare da amincewar iyayen marigayiyar.
Lamarin ya ja hankalin jama'a a fadin Najeriya, yayin da rundunar 'yan sandan Ebonyi ta mika binciken zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID), inda har yanzu ba a gano musabbabin mutuwar ba.
ADC ta jajanta wa iyalan Mary Habila tare da bukatar a gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya domin tabbatar da adalci da bayyana gaskiya ga 'yan Najeriya.
Umahi ya cike takardar takarar Tinubu
Mun ba ku labarin cewa ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa akwai nasara ga Najeriya idan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake 'dare wa karagar mulki.
Ya bayyana cewa cike fam na takarar Bola Tinubu karo na biyu mataki ne da zai kara karfafa ayyukan ci gaba da bunkasa Najeriya.
David Umahi ya bayyana haka ne bayan shugaban kasa ya bayyanar da aniyarsa na sake tsaya wa takara a babban zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng