Bidiyo: Lokacin da Tinubu Ya Mika wa Shettima Fom din Zama Abokin Takararsa a 2027

Bidiyo: Lokacin da Tinubu Ya Mika wa Shettima Fom din Zama Abokin Takararsa a 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya mika wa Kashim Shettima takardar tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa bayan APC ta amince da tikitin 2027
  • Mai taimaka wa shugaban kasa kan kafafen sada zumunta ya wallafa bidiyon taron, yana mai musanta rade-radin cewa an rage wa Shettima matsayi
  • APC ta bayyana kwarin gwiwar cewa tikitin Tinubu da Shettima zai sake samun nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika wa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, takardar tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa na jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan jam'iyyar APC ta tabbatar da Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi yadda Kiristoci suka karbi tikitin Muslim Muslim a Najeriy

Tinubu ya mika fom din takarar mataimakin shugaban kasa ga Kashim Shettima
Lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke mika fom din takarar mataimakin shugaban kasa ga Kashim Shettima. Hoto: @olabanjo_of
Source: Twitter

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan lamarin da ya kawo karshen rade-radin da aka shafe watanni ana yi kan yiwuwar shugaban kasar ya sauya mataimakinsa.

Tinubu ya mika takardar ga Shettima

An bayyana lamarin ne cikin wani bidiyo da Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Kafafen Sada Zumunta, Olusegun Dada, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

A cikin bidiyon, an ga Kashim Shettima ya isa wajen taron kafin ya yi gajeriyar tattaunawa da Shugaba Tinubu. Daga bisani shugaban kasar ya mika masa takardar da ke tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

Da yake wallafa bidiyon, Dada ya rubuta cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima takardar tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Rade-radin sauya Shettima

Bayan wallafa bidiyon, wani mai amfani da kafar sada zumunta ya tambayi Dada ko wannan ba martani ba ne ga rahotannin da suka yi ikirarin cewa an rage wa Shettima matsayi a gwamnati.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Bala Adamu ya amince ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2027

Sai dai Dada ya musanta wannan zargi, yana mai cewa babu wani lokaci da matsayin mataimakin shugaban kasa ya taba shiga cikin shakku.

Ya ce wasu mutane ne kawai ke kirkirar labarai da jita-jita ba tare da hujja ba, sannan su rika yadawa domin tayar da hankalin jama'a.

APC ta ce tana da yakinin tikitin Tinubu da Shettima zai yi nasara a zaben 2027
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

APC ta tabbatar da tikitin Tinubu da Shettima

A ranar 10 ga watan Yuli, APC ta sanar da Kashim Shettima a hukumance a matsayin mataimakin dan takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

Haka kuma APC ta karbi takardun tsayar da takarar shugaban kasa da mataimakinsa domin mika su ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin wa'adin da doka ta tanada.

Matakin mika takardar ga Shettima na kara tabbatar da cewa shugabannin APC sun kammala shirye-shiryen farko na tunkarar zaben 2027, yayin da jam'iyyar ke nuna cikakken goyon baya ga tikitin Tinubu da Shettima.

Kalli bidiyon lokacin da Tinubu ya mika fom din ga Shettima a kasa:

Martanin Kiristoci kan Tinubu/Shettima

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata kungiyar Kiristoci a yankin Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki.

Kara karanta wannan

Yadda Kashim Shettima ya sharbi kuka a lokacin da Buhari zai rasu a asibiti

Shugaban kungiyar, Fasto Jolly Usman, ya ce ƙwarewar Shettima da haɗin gwiwarsa da Tinubu sun taimaka wajen inganta tsaro.

Ƙungiyar ta bukaci 'yan Najeriya su yi hukunci kan shugabanni bisa ayyukansu da nagartarsu, ba wai la'akari da bambancin addini kaɗai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com