Shettima Ya Kai wa Tinubu Ziyara bayan APC Ta Tabbatar da Shi a Tikitin 2027
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sa labule da shugaba Bola Ahmed Tinubu jim kadan bayan an tabbatar masa kujerarsa a takarar 2027
- A ranar Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2026 ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen rade-radin wanda zai zama abokin takararsa a zabe mai zuwa
- An jima ana rade-radin cewa bai dace Tinubu ya tafi da Shettima ba domin a ba wa kirista dama ya zama mataimakin shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ziyara a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2026.
Ziyarar ta biyo bayan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a Abuja, inda aka bayyana tikitin Tinubu-Shettima a hukumance domin tunkarar babban zaben shekara ta 2027.

Kara karanta wannan
Albarkacin Shettima, matasan Arewa sun yi wa Tinubu alkawarin ruwan kuri'u a 2027

Source: Twitter
Jaridar The Cable rahotanni sun ce Shettima ya je fadar shugaban kasa ne domin nuna godiya ga Tinubu bisa ci gaba da ba shi damar kasancewa abokin takararsa.
Tinubu zai tafi da Shettima
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa an kawo karshen rade-radin da aka shafe makonni ana yi kan ko APC za ta ci gaba da tafiya da Shettima a matsayin mataimakin dan takararta.
Da wannan mataki, APC za ta sake shiga zaben shugaban kasa na 2027 da irin tawagar da ta ba ta nasara a zaben 2023, wato tikitin Muslim-Muslim da wasu ke adawa da shi.
Tun da farko a ranar Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2026 mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama'a, Sunday Dare, ya sanar da cewa Tinubu ya mika takarda a kan Kashim Shettima.
Abinda ya kai Shettima wajen Tinubu
Rahotanni sun bayyana cewa Kashim Shettima ya kai ziyarar girmamawa da godaiya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na sake zabensa.

Kara karanta wannan
Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027

Source: Facebook
Zabensa a tikitin takarar 2027 na zuwa bayan rade-radin da ake yi cewa akwai yiwuwar za a ajiye Kashim Shettima domin a sirka Muslim-Muslim tsakanin shugaba da mataimakinsa.
Haka kuma an ji yadda wasu daga cikin makusanta suka rika shaida wa Tinubu cewa Shettima na neman ganin bayansa, lamarin da ya jawo tsoron samun sabani a tsakaninsu.
Kashim ya zama abokin takarar Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen duk wata jita-jita da jama'a ke yaɗa wa kan wanda zai dauka a matsayin abokin takara a babban zaben 2027.
Rahotanni sun nuna cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta karbi takardun tsayawa takarar Tinubu da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa da za su tunkari zaben da ke tafe nan da 'yan watanni.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da Abba Kabir Yusufa na Kano na cikin gwamnonin da suka halarci taron da APC ta shirya a Abuja yayin da ake ci gaba da shirin siyasar 2027.
Asali: Legit.ng