Albarkacin Shettima, Matasan Arewa Sun Yi wa Tinubu Alkawarin Ruwan Kuri'u a 2027

Albarkacin Shettima, Matasan Arewa Sun Yi wa Tinubu Alkawarin Ruwan Kuri'u a 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya sake tabbatar da amincewarsa ga Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimakin shugaban ƙasa a 2027
  • Kabiru Garba Kobi, wani shugaban matasan APC ya ce Arewa maso Gabas za ta saka wa Tinubu da ruwan ƙuri'u saboda sake ba Shettima tikiti
  • Shugaban matasan ya nemi masu adawa da Shettima su mayar da wuka cikin kube, su haɗa kai domin tabbatar da nasarar Tinubu da APC a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - Wata kungiyar matasan jam'iyyar APC a Arewa maso Gabas, ta yi wa Shugaba Bola Tinubu godiya bisa sake zabar Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi, ya bugi kirji da cewa, Arewa maso Gabas za ta mayar da bikin wannan alheri ta hanyar yiwa Tinubu ruwan kuri'u a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027

Matasan Arewa maso Gabas sun yi alkawarin yi wa Tinubu ruwan kuri'u saboda Shettima.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu), Kabiru Kobi, shugaban kungiyar matasan APC (tsakiya), da Kashim Shettima (dama). Hoto: @officialABAT, @KashimSM
Source: Twitter

Arewa za ta yi wa Tinubu ruwan kuri'u

A zantawarsa da Legit Hausa, Kabiru Garba Kobi ya ce abin da Tinubu ya yi na sake zabar Shettima matsayin abokin takararsa ya nuna cewa yana girmama Arewa maso Gabas.

A cewar Kabiru Kobi, a yanzu Arewa gaba daya ta yarda cewa Kashim Shettima ya na sonta tun da har ya ki amincewa da duk wani matsin lamba na sauya Kashim Shettima.

"Na farko dai, al'ummar Arewa a yanzu da nake maka magana, ina wajen wata maciya ne, inda ake yanka dabbobi, ake murna da wannan abu. Arewa sun yi farin ciki, yanzu ne suka gane Tinubu masoyin Arewa ne.
"Kuma tun da ya yi mana wannan halacci, to ya kwantar da hankalinsa, in Allah ya yarda, mu zamu kawo masa fiye da kuri'un da ya samu a zaben baya.
"Ba don komai ba, don ya kaunaci mai kaunar mu, don ya dauki wanda yake dawainiya da mu, wanda yake son Arewa maso Gabas."

Kara karanta wannan

Baki abin magana: Sanata Ndume ya yi maganganu bayan ganawa da Tinubu

- Kabiru Garba Kobi.

Tasirin kujerar Shettima ga Arewa maso Gabas

Shugaban kungiyar matasan jam'iyyar APCn ya kuma yi nuni da cewa, kujerar mataimakin shugaban kasa da ke a hannun Kashim Shettima na da matukar tasiri ga Arewa maso Gabas.

Kabiru Garba Kobi ya ce:

"Mu dawo maganar yankina Arewa maso Gabas, ita ce shiyyar da tun bayan mulkin Obasanjo ba a taba bamu mataimakin shugaban kasa ba, sai a mulkin Tinubu, an ba mu kuma an sake bamu, don haka muna godewa Allah.
"Don haka ya zama wajibi mu saka halacci da halacci. Za mu yi Tinubu kwan mu da kwarkwatarmu, za mu yi sadaka, za mu addu'a, za mu fito shago shago, mu fadi dalilanmu na zaben Tinubu.
"Kuma in Allah ya yarda, karfin karfe 10:00 na safe Tinubu ya ci zabe."
Kabiru Kobi ya nemi dukkan masu adawa da Shettima da su hakura yanzu su zo su hada kai don nasarar APC.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da shugaban kungiyar matasan APC, reshen Arewa maso Gabas, Kabiru Kobi. Hoto: @officialSKSM/X, UGC
Source: UGC

Sakon Kabiru Kobi ga 'yan adawar Shettima

Kabiru Garba Kobi, ya kuma kira ga wadanda a baya suka nuna adawa da sake ba Shettima tikitin takarar mataimakin shugaban kasa, yana mai cewa yanzu lokaci ya yi da za a hada kai don ciyar da kasa gaba.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Ya bayyana cewa:

"Muna gaya masu cewa, wannan mutumin shuri ne ajiyar Allah, duk abin da Allah ya ajiye ka yi yunkurin cirewa za ka ji kunya. Mu yanzu ba mu da lokacin rigima da su, mu zo mu hada kai, mu yi yaki tare don ganin Shugaba Tinubu ya yi nasara"

Kabiru Kobi ya shaidawa shugaban kasa Tinubu cewa nan da sati daya zai ga canji a harkar siyasar Arewa maso Gabas, don nuna godiyarsu ga tikitin mataimakinsa da ya sake ba Shettima.

Kobi ya yi wa Babachir kaca-kaca

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar matasan APC, reshen Arewa maso Gabas (APC-YPNE) ta caccaki Babachir Lawal saboda kalamansa kan Kashim Shettima.

Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi ya zargi Babachir da raina Shettima tare da nuna kiyayyarsa a fili kan tikitin Muslima Muslmi na 2023.

A zantawarsa da Legit Hausa, Kobi ya ce hassada ce kawai ke cin Babachir, kuma yana ji yana gani Shettima zai kara daukaka a gwamnatin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com