INEC Ta Sanya Karin Kudi cikin Abubuwan da Take Bukata kafin Zaben 2027
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya buƙaci RMAFC ta amince da ƙarin kuɗaɗe domin shirye-shiryen zaɓen 2027
- Farfesa Amupitan ya ce gudanar da zaɓen gwamna yanzu ya fi tsadar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya
- Shugaban na hukumar INEC ya ce inganta jin daɗin ma'aikata da saka hannun jari a fasaha da horo zai ƙarfafa sahihancin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya mika bukatarsa ga hukumar RMAFC mai kula da rarraba kudade.
Farfesa Amupitan ya buƙaci hukumar RMAFC ta amince da ƙarin kuɗaɗe tare da tabbatar da ci gaba da tallafa wa INEC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 14 ga watan Yulin yayin wata ziyara ta musamman da ya kai wa shugaban RMAFC, Dakta Mohammed Bello Shehu, a Abuja, cewar wata sanarwa a shafin Facebook na INEC.

Kara karanta wannan
Gwamna ya zakulo samari da zawarawa 300, zai masu auren gata da sadakin N250000 a Kebbi
INEC ta bayyana nauyin da ke kanta
Shugaban INEC ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ɗora wa hukumar nauyin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, 'yan Majalisar Tarayya, gwamnoni, 'yan majalisun dokokin jihohi da kuma shugabannin ƙananan hukumomin Abuja.
Ya ƙara da cewa ayyukan hukumar INEC sun kuma haɗa da ci gaba da rajistar masu zaɓe da kuma rajistar jam'iyyun siyasa.
Tsadar gudanar da zaɓe ta ƙaru
A cewarsa, kuɗin gudanar da zaɓen gwamna guda ɗaya yanzu ya zarce jimillar kuɗin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya.
Ya ce INEC ce ke ɗaukar nauyin shari'o'in da suka shafi zaɓe kafin zaɓe da bayan zaɓe, ciki har da ƙorafe-ƙorafen da ke tasowa daga zaɓen fidda gwani na jam'iyyun siyasa.
Farfesa Amupitan ya bayyana cewa hukumar na da ofisoshi a jihohi 36, babban birnin tarayya da kuma dukkan ƙananan hukumomi 774, kuma gwamnatin tarayya ce ke ɗaukar nauyin tafiyar da wannan tsari a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha kaye," An yi hasashen gwamnan da zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027
An nemi a inganta jin daɗin ma'aikata
Shugaban INEC ya kuma yi kira da a inganta albashi da sauran alawus na ma'aikatan hukumar wadda ke kula da zabubbuka.
Ya ce biyan ma'aikata albashi mai gwabi yana da matuƙar muhimmanci wajen riƙe ƙwararrun ma'aikata da tabbatar da ingancin aiki.
A cewarsa, hukumar ta rasa wasu gogaggun ma'aikata da suka bar ƙasar saboda ƙarancin albashi.
Ya ce inganta walwalar ma'aikata zai ƙara musu ƙwarin gwiwa tare da ƙarfafa amincewar jama'a da sakamakon zaɓe.
INEC ta nemi ƙarin jari a fannin fasaha
Farfesa Amupitan ya kuma buƙaci a ƙara kuɗaɗe domin gina ababen more rayuwa, inganta fasahar zaɓe da horar da ma'aikata.
Ya ce irin wannan saka hannun jari zai taimaka wajen adana ƙwarewa da gogewar da hukumar ta tara tsawon shekaru.

Source: Facebook
A ƙarshe, ya tabbatar wa RMAFC cewa INEC za ta ci gaba da ƙoƙarin gudanar da zaɓe cikin 'yanci, adalci, gaskiya da sahihanci.
Ya kuma bayyana cewa an tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Kara karanta wannan
2027: Atiku ya kawo hujjoji, ya zargi Tinubu da naɗa wanda zai ruguza 'yan adawa a INEC
ADC ta bukaci INEC ta binciki Nafiu Bala
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bukaci hukumar zabe ta INEC da ta binciki Nafiu Bala Gombe kan zargin amfani da takardun bogi.
ADC mai adawa a Najeriya ta bayyana cewa, tsagin Nafi'u Bala Gombe na yada karya da nufin rikitar da jama'a gabanin zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng