ADC Ta Bukaci INEC Ta Binciki Tsagin Nafi'u Bala kan Zargin Takardun Bogi
- Jam'iyyar hadakar yan adawa ta ADC ta bukaci hukumar zabe ta INEC ta binciki zargin jabun takardu da wata tsagin jam'iyyar ke amfani da su
- Jam'iyyar ta ce shugabancin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta amince da shi ne kaɗai ke da damar shiga tsarin shigar da sunayen 'yan takara
- ADC ta ce ta riga ta shigar da sunayen Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi a shafin INEC, tare da kira ga jama'a su yi watsi da ikirarin tsagin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'iyyar hadakar adawa ta ADC ta bukaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da bincike kan zargin tsagin Nafi'u Bala ya yi amfani da takardun INEC na bogi.

Kara karanta wannan
Ana neman rusa takarar Atiku, INEC ta yi magana kan sunayen 'yan takara na tsagin ADC
Jam'iyyar ta yi wannan kira ne bayan tsagin da Nafiu Gombe ke jagoranta ya yi ikirarin cewa ta shigar da sunayen ɗan takarar shugaban ƙasa da sauran 'yan takara a shafin karɓar sunayen 'yan takara na INEC.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin 13 ga watan Yuli, 2026.
Jam'iyyar ADC ta mika koke ga INEC
Jaridar The Cable ta wallafa cewa jam'iyyar ADC ta kara da cewa, tsagin Nafi'u Bala na yada karya da nufin rikitar da jama'a gabanin zabe mai zuwa.
Jam'iyyar ta ce shugabancin da INEC ta amince da shi ne kaɗai ke da damar shiga shafin karɓar sunayen 'yan takara, kuma shi ne ya kammala aikin miƙa sunayen bisa tanadin dokar zaɓe.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce:
"INEC ba ta bai wa shugabancin da ba ta amince da shi damar shiga shafin karɓar sunayen 'yan takara ko lambar shigar da sunaye ba. Haka kuma, hukumar ba ta ba jam'iyya guda lambobi biyu. Idan hakan zai yiwu, kowa zai iya shigar da sunaye ya ce shi ne halastaccen shugabancin jam'iyya. Wannan ba haka doka ko tsarin INEC yake aiki ba."
ADC ta kalubanci Nafi'u Bala
ADC ta ƙalubalanci tsagin da ya gabatar da hujjar da ke nuna cewa ya samu damar shiga shafin INEC domin shigar da sunayen 'yan takara.
Har ila yau, ADC ta bukaci INEC ta binciki abin da ta bayyana a matsayin jabun takardu da kuma amfani da takardun da aka ce daga hukumar suka fito ba tare da izini ba.
Ta ce:
"Mun ja hankalin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa kan abin da ya yi kama da takardun jabu da kuma amfani da takardun da aka ce daga hukumar suka fito ta hanyar da za ta iya haifar da ruɗani tare da lalata amincewar jama'a da mutuncin hukumar. Muna da yaƙinin cewa hukumar za ta binciki wannan batu tare da ɗaukar matakan da suka dace."
Tsagin ADC ya fitar da yan takara
A wani labarin, kun ji cewa tsagin jam'iyyar ADC na Nafiu Bala ya kammala daura sunayen 'yan takararta a shafin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC don zaben 2027 mai zuwa.
Farfesa Chris Uba daga jihar Anambra ne aka zaba a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a bangaren Nafiu da Dr. Shamsuddin Modibbo Barkindo dan jihar Adamawa ne aka zaba a matsayin mataimakin dan takarar.
A cikin sanarwar da ya fitar, Nafi'u Bala ya bayyana cewa an sanya sunayen 'yan takara a hukumance, bayan na dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa an sanya na 'yan takarar majalisar dokoki.
Asali: Legit.ng

