"Tinubu Zai Sha Kaye," An Yi Hasashen Gwamnan da Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027

"Tinubu Zai Sha Kaye," An Yi Hasashen Gwamnan da Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027

  • Jam'iyyar APM ta sake tabbatar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na a zaben 2027
  • APM ta tabbatar da cewa ta tura sunayen Makinde da sauran 'yan takararta zuwa shafin INEC bayan karbar lambobin shigar da bayanai
  • Jam'iyyar adawan ta yi ikirarin cewa Gwamna Makinde ya fi duka yan takara cancanta kuma zai kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar APM ta bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takararta na shugaban ƙasa, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, zai yi nasara a zaɓen 2027.

Jam'iyyar ta ce tana ganin Makinde ya samu karɓuwa a wurin 'yan Najeriya a matsayin wanda zai gaji shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Sayi Makinde lokacin da aka tabbatar da shi a matsayin dan takarar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Rahoton Leadership ya ce APM ta sanar da cewa ta yi nasarar shigar bayanan Makinde da sauran 'yan takararta na zaɓen 2027 a shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Kara karanta wannan

Ana neman rusa takarar Atiku, INEC ta yi magana kan sunayen 'yan takara na tsagin ADC

APM ta ce ta cika ƙa'idojin INEC

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, sakataren yaɗa labarai APM na kasa, Abubakar Yusuf, ya ce an yi nasarar tura bayanan ɗan takarar shugaban ƙasa, mataimakinsa, da kuma 'yan takarar Sanata da na Majalisar Wakilai.

Ya ce APM ta kuduri aniyar lashe zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓuka, tare da ƙara faɗaɗa yaɗuwarta a matakin ƙasa da tabbatar da cewa 'yan takararta sun samu karɓuwa.

Yan siyasa na ci gaba da shiga APM

A cewarsa, APM na ci gaba da samun sababbin mambobi da magoya baya saboda ganin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun shiga cikinta.

Abubakar ya ce:

"Mun tura bayanan ɗan takararmu na shugaban ƙasa, mataimakinsa da kuma 'yan takarar Majalisar Dokoki kamar yadda INEC ta buƙata. Wannan wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarinmu na bai wa 'yan Najeriya zaɓi nagari a zaɓen 2027."

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci INEC ta binciki tsagin Nafi'u Bala kan zargin takardun bogi

A cewarsa, 'yan takarar APM mutane ne masu nagarta, gaskiya da kuma kyakkyawan tarihi a fannoni daban-daban, waɗanda za su iya samar da shugabanci na gari, cewar rahoton Gurdian.

Makinde ya cancanci shugabanci

Abubakar Yusuf ya ce matsalolin tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da durƙushewar tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya na buƙatar sabon shugabanci.

Ya ce:

"A gwamnatin APM ƙarƙashin jagorancin Makinde, jin daɗin 'yan Najeriya zai kasance a sahun gaba wajen tsara manufofin gwamnati.
"Makinde ya dace da mulkin Najeriya duba da yadda ya nuna ƙwarewa wajen gudanar da mulki da kula da dukiyar jama'a.
"Ya haɗa gogewa da kuzari, hangen nesa da kuma ikon haɗa kan 'yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin siyasa, ƙabila ko addini ba."
Makinde.
Gwamna Makinde lokacin da ya karbi tutar takarar shugaban kasa daga hannun shugabannin APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

APC ta nemi Makinde ya yi murabus

A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen Oyo ta bukaci Gwamna Seyi Makinde ya yi murabus daga mukaminsa idan har yana ganin ba shi da ikon kare rayuka.

APC ta duki wannan mataki ne biyo bayan kalaman da Makinde ya yi yayin jawabin karɓar takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APM a Ibadan.

APC ta yi watsi da ikirarin Makinde cewa yana fuskantar ƙalubale wajen magance matsalar tsaro saboda dukkan tsarin tsaro yana ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262